BBC Hausa of Friday, 30 April 2021

Source: BBC

Usman Bugaje ya gamu da fushin DSS saboda caccakar Buhari

An kama Dr Usman Bugaje ne saboda ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari An kama Dr Usman Bugaje ne saboda ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari

Masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya musamman shafin Twitter sun fusata sakamakon matakin da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta dauka na gayyatar Dr Usman Bugaje saboda ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Dr Bugaje, wanda ya yi hira da gidan talbijin na AIT a makon nan, ya caccaki gwamnatin Buhari bisa gazawarta wajen tabbatar da tsaro a kasar musamman a Arewa.

Ya yi kira ga shugaban kasar da 'yan majalisun dokokin tarayya su sauka daga mukamansu idan ba za su iya tabbatar da tsaro a kasar ba.

"Idan ba za ku iya gyara matsalolin kasar nan ba, ya kamata ku sauka daga mulki. Me kuke yi a kan mukamanku? Su ma 'yan majalisar dokoki, suna zaune suna jin dadin albashi da sauran alawus-alawus yayin da kasar nan take rugujewa kuma babu abin da suke yi. Wannan kasar tana rugujewa amma kuna nan a zaune kuna ta bayar da uzuri," in ji Dr Bugaje.

Wadannan kalamai sun jawo masa gayyata daga hukumar DSS inda wasu rahotanni suka ce ya kwashe tsawon wunin Laraba yana amsa tambayoyi.

Masu lura da lamura da sharhi kan ci gaban Najeriya irin su Dr Mairo Mandara sun kwashe tsawon ranar suna jiran ganin an saki dan siyasar, wanda da shi aka kafa jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

Ba wannan ne karon farko da fitaccen masanin yake sukar gwamnatin Shugaba Buhari ba saboda abin da ya kira gazawarta wajen tabbatar da tsaro a kasar.

Dr Bugaje, wanda dan asalin jihar Katsina ne da ke fama da hare-haren 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane, ya taba samun gayyata daga wurin Shugaba Buhari domin ya zama jakadan Najeriya a wata kasa amma ya ki karba yana mai cewa ci gaban arewacin Najeriya ne babban abin da zai sanya a gaba.

Me 'yan Twitter suke cewa?

Gayyatar da DSS ta yi wa dan siyasar ta haifar da suka daga masu amfani da Twitter inda sunan Usman Bugaje ya kasance daya daga cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a shafin.

Da yake tsokaci kan batun, fitaccen mai sharhin nan kan harkokin yau da kullum, Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce "gwamnatin [Buhari] tana yi wa kanta babbar illa saboda yadda take tsare da kuma musgunawa masu sukarta. Mun dade muna yaki domin tabbatar da 'yancin jama'a kuma babu wanda ya isa ya rufe mana baki."

A nata bangaren, 'yar Kafanchan, ta koka kan yadda mutane suke yin shiru yayin da Buhari yake "hukunta 'yan arewa da suka soki" gwamnatinsa tana mai cewa a bara ma sai da jami'an tsaro suka tsangwami matarsa saboda ta bayyana ra'ayinta kan matsalolin da kasar take ciki.