BBC Hausa of Sunday, 18 April 2021

Source: BBC

Waiwaye: Dawowar Buhari daga Landan da Kashe kwamandojin ISWAP 18

Shugaba Buhari ya sha yin irin wannan tafiya don jinya ko duba lafiyarsa Shugaba Buhari ya sha yin irin wannan tafiya don jinya ko duba lafiyarsa

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 10 ga Afirilu zuwa Asabar 17 ga Afirilu.

An bude wannan makon ne da labarin ganin watan Ramadana a Najeriya, kamar yadda aka saba duk shekara majalisar sarkin musulmai na zama domin karbar bayanai daga wadanda suka ga watan a jihohinsu.

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Sultan Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin jinjirin Watan Ramadan a Najeriya.

A wani jawabi da ya gabatar, Sarkin Musulmin ya ce an ga jinjirin watan na Ramadana a daren Litinin, inda ya ce Litinin din 12 ga watan Afirlun 2021 ce ranar karshe ta watan Sha'aban na Shekarar Hijira ta 1442.

Sannan ya ce Talata 13 ga watan Afrilun 2021 ce ranar farko ta watan Ramadana na Shekarar Hijira ta 1442.

"Ƴan uwa al'ummar Musulmi, bisa ga sharuddan Musulunci, muna sanar da ku cewa yau Litinin 29 ga watan Sha'aban shekara ta 1442 bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 12 ga watan Afrilun shekarar 2021, an kawo karshen watan Sha'aban na shekara ta 1442," in ji Sarkin Musulmi.

Cika shekaru 7 da sace 'yan matan Chibok

Ya yin da ake jimamin cika shekara 7 da sace 'yan matan makarantar Chibok a Najeriya Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya ce za za a ceto sauran 'yan matan da ma sauran mutanen da aka sace daga jihar cikin koshin lafiya.

Zulum ya fadi hakan ne a cikin wani bayaninsa na cikar shekara bakwai da mayakan Boko Haram suka sace daliban na makarantar mata ta Chibok lokacin da suke gab da rubuta jarrabawarsu ta karshe.

Duk da cewa an sako wasu daga cikin daliban to amma har yanzu akwai da dama wadanda suka rage a hannun kungiyar ta Boko Haram.

Zulum ya ce a matsayinsa na uba, yana jin takaicin kuncin da iyayen ke ciki tsawon shekara bakwai yaransu na hannun 'yan bindiga.

Sasanta Dangote da BUA da Gwamnan Kano ya yi

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sasanta tsakanin hamshaƙan ƴan kasuwar Najeriyar nan biyu ƴan asalin jihar, Alhaji Aliko Ɗangote da Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi'u kan saɓanin fahimtar da suka samu a baya-bayan nan.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamnan Ganduje ya ce an yi zaman sulhun ne tsakanin jami'an gwamnatin jihar da wasu manyan masu faɗa a ji da kuma ƴan kasuwar ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce rikicin na baya-bayan nan ya samo asali ne tsakanin manyan masu arzikin biyu kan batun farashin sikari a kasuwar Najeriya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Dangote ya zargi BUA da amfani da wata dama ta hanyar da ba ta dace ba, yayin da shi kuma Abdussamad ya ce yana so ya mamaye kasuwar ne ya kuma dinga sa farashi yadda ya ga dama.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a makon da ya gabata, Dangote ya yi watsi da zargin sanya farashin da ya ga dama.

Dawowar Buhari daga Landan

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koma Najeriya daga London a ranar Alhamis da yamma bayan shafe makonni biyu.

Mai taimaka wa shugaban kan yada labarai Malam Garba Shehu ne ya tabbatar wa da BBC labarin.

Shugaba Buhari ya tafi birnin Londan da ke kasar Birtaniya ne ranar 30 ga watan Maris domin a duba lafiyarsa.

Manyan jami'an gwamnatin ƙasar da shugabannin rundunonin tsaro da wasu ministoci na daga cikin waɗanda suka tarbi shugaban a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Shugaba Buhari ya sha yin irin wannan tafiya don jinya ko duba lafiyarsa, "don haka ba sabon abu ba ne," kamar yadda Garba Shehu ya fada gabanin tafiyar shugaban.

Kashe kwamandojin ISWAP 18 da sojin Najeriya suka yi

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe wani babban kwamandan kungiyar ISWAP mai suna Bukar Gana wanda ake kira da Abu Asiha, tare da wasu mayakansa wadanda suke shirin daukar fansa a yankin Damasak, bayan wani dauki ba dadi da suka yi da sojin Najeriya a ranar Alhamis.

Cikin wata sanarwa da kakain rundunar Mohammed Yerima ya fitar a wanar Juma'a ta ce, an kuma ta yin lugudan wuta ta sama a yankunan da maharan ke boyewa a yankuna irinsu Kusuma da Sigir a de ke Ngala da Arijallamari.

Hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar manyan kwamandojin kungiyar irinsu Mohammad Fulloja da Ameer Mallam Bello da Ba'a kaka Tunkushe, da Abu Muktar Al -Ansari, Ameer Abba Kaka, sai kuma Abu Huzaifa, da Ameer Modu Kwayem, yayin da Goni Mustapha wanda shi ne limmamin ISWAP din ya tsere da harsashi a jikinsa.

Matakin CBN na daina ba da tallafin sikari da Alkama

Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce kasar ba za ta kara bai wa masu shigo da sikari da alkama kudaden kasar waje.

Najeriya wadda ita ce mafi yawan al'umma a Afirka, kuma jagaba ta fuskar karfin tattalin arziki, ta dogara da shigo da abincin da ta ke ciyar da sama da 'yan kasar miliyan 200 daga kasashen ketare.

Babban bankin Najeriyar ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Sikari da alkama za su shiga cikin jerin kayan da za a haramta shigo da su Najeriya. Ya kamata mu yi aiki tare dan ganin an fara samar da su a cikin gida maimakon shigo da su daga kasashen ketare".