BBC Hausa of Sunday, 30 May 2021

Source: BBC

Waiwaye: Nada sabon shugaban sojin kasa da bikin abaya a KUST

An nada sabon shugaban hafsan sojojin Najeriya Majo Janar Faruok Yahaya An nada sabon shugaban hafsan sojojin Najeriya Majo Janar Faruok Yahaya

Barkewar cutar amai a Bauchi

Hukumomi a jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya sun ce wata cuta mai kama da kwalara da ta ɓarke a jihar ta yi ajalin kimanin mutum 20.

Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Aliyu Muhammad Maigoro ya shaida wa BBC cewa fiye da mutum 320 suka kamu da cutar ta amai da gudawa.

Ya ce cutar ta bazu a yankunan kananan hukumomi tara, tun daga makwanni biyu da suka gabata.

An dai danganta barkewar annobar da gurbatar ruwan da jama'a ke sha sakamakon zubar ruwan saman farko.

Kwamishinan ya ce an kafa kwamiti na kar ta kwana don dakile cutar.

Rage darajar Naira da CBN ya yi

Babban bankin Najeriya ya karya darajar Naira da kashi 7.6 cikin 100 kan dalar Amurka a dai-dai lokacin da ƙasar ke shirin amfani da dalar Amurka kawai wajen auna kadarin kuɗinta.

Babban bankin ya karya darajar daga Naira 370 ga dala 1 da ake amfani da shi a hukumance a sabon tsarin canji na Nigerian Autonomous Foreign Exchange (NAFEX), wanda a yanzu ya kai naira 410.25 ga dala 1 a cewar bankin.

Bankin ya bayyana sauyin a shafinsa kuma gwamnan bankin Godwin Emefiele ya bayyana cewa "mun gano cewa an daina sauya Naira da farashin da CBN a hukunmance, don haka yanzu muna sa ido kan kasuwar kuma shi ya sa muka dauki wannan matakin."

Bikin abaya da aka yi a Jami'ar KUST a Kano

Hukumar gudanarwa ta Jami'ar Fasaha Ta Wudil da ke jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya (KUST Wudil), ta umarci dukkan ɗalibai mata na makarantar su sanya abaya a ranar Alhamis, inda suka ayyana ranar a matsayin Ranar Abaya.

Wasu ɗaliban makarantar sun tabbatar wa BBC cewa mataimakin shugaban jami'ar mai kula da sha'anin mulki da kuma shugaban tsangayar kula da al'amuran ɗalibai ne da kansu suka sanar da hakan ga ɗaliban.

Wata ɗaliba da ta buƙaci BBC ta sakaya sunanta ta ce "tawagar hukumar makaranta da kanta ta je har hostel don sanar da mu wannan mataki."

Hukumar makarantar ta ɗauki wannan mataki ne bayan bayyanar wani bidiyo da ke nuna yadda wasu ɗalibai maza suke cin zarafin wata ɗalibai da ke sanye da abaya tare da yi mata ature da ihun "mai abaya, mai abaya," al'amarin da ya sa ta muzanta a cewar wasu ɗalibai.

Kammala jin ra'ayin jama'a kan gyaran kundin tsarin mulki da Ministoci suka yi

A Najeriya, a ranar Alhamis ne `yan Majalisar Dattawan ƙasar suka kammala sauraron ra`ayin jama`a game da gyaran fuskar da suke so a yi wa kundin tsarin mulkin kasar.

An yi zaman ne a shiyyoyi shida na kasar kuma ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da dama sun gabatar da bukatunsu.

Birnin Kaduna na cikin wurare 12 da tawagar `yan majalisar suka yi zama don tattara ra`ayoyin `yan kasar, kuma a nan ne wakilai daga jihohin Kaduna da Kano da Jigawa da kuma Katsina suka gabatar da nasu bukatun.

Mafi yawan bukatun dai sun karkata ne ga batun saka wa ƙananan hukumomi da ɓangaren shari`a mara.

Sai kuma masu bukatar a kirkiri sabbin jihohi da maganar samar da daidaito da inganta rayuwar mata.

Kara gano gawar mutum 60 da jirgi ya kife da su a Jihar Kebbi

Ya yin da aka shiga rana ta biyu na aikin neman waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a jihar Kebbi, ya zuwa yanzu an gano gawar mutum 60.

A jiya Laraba ne jirgin ya rabe gida biyu ɗauke da fasinjoji fiye da 100, lamarin da ya yi sanadiyar nutsewarsa.

Kawo yanzu mutum 22 ne hukumomin jihar suka ce sun tsira da rayukansu.

Sai dai mutum fiye 100 ne suka rasu a hatsarin, yayin da har yanzu ba a san inda fiye da 50 suke ba.

Naɗa sabon babban hafsan sojin ƙasan a Najeriya

Buhari ya naɗa Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya.

Rundunar sojin ƙasar ce ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita a yau Alhamis.

Naɗin na zuwa ne kwana shida bayan rasuwar Janar Ibrahim Attahiru mai jagorantar rundunar.

Janar Attahiru ya rasu ne a wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a Kaduna, da kuma wasu mutum 11 cikin har da janar-janar uku.

Alkawarin ara daukar 'yan N-Power miliyan daya a Najeriya da Gwamnatin Buhari ta yi

Ministar ayyukan jin kai ta Najeriya Sadiya Farouq ta ce gwamnati za ta dauki 'yan N-Power miliyan daya a fadin Najeriya a nan gaba.

Ministar ta bayyana hakan ne a wani a wani taron wayar da kai da ya gudana a Abuja kan yadda 'yan jarida za su rika gudanar da ayyukansu.

Yayin taron ta ce "za a dauki mutum miliyan daya karkashin shirin N-Power a matsayin rukuni na C karkashin shirin taimakawa al-umma.

Tun a ranar ma'aikata ta duniya shugaba Buhari ya sanar da shirin gwamnatinsa na ninka yawan mutanen da ke amfana da shirn N-Power daga 500,000 zuwa miliyan daya.

Sadiya ta ce tsarin N-Power da sauran da aka fio da su an kirkire su ne da nufin yakar rashin aikin yi da matsalar tsaro a Najeriya.

Hana karatu da IPOB ta yi da sauran harkoki a Imo ranar Juma'a

Makarantu da wasu wurare da dama a Owerri, babban birnin jihar Imo sun kasance a rufe a yau.

Hakan ya biyo bayan umarnin da kungiyar nan da ke neman ficewa daga Naijeriya ta Biafra da aka fi kira da IPOB ta nemi a yi

Ta nemi a yi hakan domin nuna juyayi da alhini sakamakon mutuwar daya daga cikin manyan komandojin kungiyar Biafra da ake kira Okonso da jami'an tsaron Naijeriya suka kashe a kwanan nan.

Ana dai ci gaba da zaman dar-dar a daukacin yankin kudu maso gabashin kasar.

Rahoton da ke cewa an yi wa mutum '411 fyade a Sokoto cikin shekara daya'

Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya ta ce an yi wa mutum 411 fyade a cikin shekara guda a jihar.

Kwamishinar mata da al'amuran yara ta jihar, Hajia Kulu Sifawa ce ta shaida haka a lokacin bikin ranar yara da aka gudanar a wannan makon a Najeriya.

Ta shaida wa BBC cewa lamarin ya hada da matan da aka ci zarafinsu ta hanyar lalata da kuma maza da aka yi luwadi da su.

"Mun bude cibiya da ake kira Nana Khadija inda ake kai wadanda aka yi wa fyade( domin a duba lafiyarsu), kuma muna da alkaluman wadanda aka yi wa fyade ko cin zarafi: ina nufin luwadi da ake yi a maza wadanda aka kai kara," in ji ta.

Kiraye-kirayen a raba Jihar Kaduna

Wasu al'ummomi a Najeriya daga bangarori daban-daban na ta shirye-shiryen gabatar da kudurorinsu a game da shirin kawo gyara ga kundin tsarin mulkin kasar.

A jihar Kaduna, maganar ta yi nisa wasu daga cikin al'ummomin kudancin jihar na nuna neman a ba su nasu bangaren a yayin da wasu daga cikin yan kudancin ke cewa har yanzu basu da cancantar a ce sun balle daga Kaduna.

Johnathan Osake shugaban kungiyar yan kudancin Kaduna wato SOKAPU ya yi wa BBC karin bayani game da hujarsu:

"Kudancin Kaduna da bangaren arewacinsa an dade ana rashin zaman lafiya. Al'adunmu da daban, kuma mun san cewa idan aka raba jihar, kowa yaje yana cin gashin kansa, gaskiya zai kawo zaman lafiya."