Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 18 ga Afirilu zuwa Asabar 24 ga Afirilu.
Gargadin Buhari ga 'yan bindiga
A cikin makon da ya gabata ne, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi 'yan bindigar da ke kashe-kashe musamman a arewacin kasar kan cewa "Su shiga hayyacinsu, su daina jin cewa gwamnati ba za ta iya maganinsu ba".
Buhari ya yi wannan gargadin ne a ranar Alhamis yayin da yake Allah-wadai da kisan da 'yan bindigar suka yi wa mutane sama da 50 a kauyukan Zamfara.
Shugaban wanda ya yi gargadin cewa "Za a kawo karshen Irin wannan rashin girmama rayuwar mutanen da 'yan bindigar ke yi a kusa ba da dadewa ba", ya kara da cewa, "Dole mu dakatar da wannan kisan da ake yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba",
Ƴan sandan Najeriya da aka kai Somaliya domin samar da tsaro
Kazalika a cikin makon ne dai wata tawagar ƴan sandan Najeriya mai ƙunshe da 'yan sanda 144 ta isa ƙasar Somalia domin aikin wanzar da zaman lafiya.
Tawagar, wadda ke karkashin shirin Tarayyar Afirka na samar da zaman lafiya a Somalia da a takaice ake kira (AMISOM), ta isa kasar ne tun ranar Asabar.
Sanarwar da Tarayyar Afirka ta wallafa a shafinta na intanet ta ce ƴan sandan za su kwashe shekara guda suna aiki a Somalia, wadda ke fama da hare-haren mayakan ƙungiyar Al-Shabaab.
"A shekara ɗayan da za su yi za su bayar da shawarwari da kuma dabaru na aiki ga rundunar ƴan sandan Somaila," in ji sanarwar.
Zargin da Najeriya ta yi wa Birtaniya na bai wa yan IPOB da MASSOB mafaka
Ministan watsa labaran Najeriya Lai Mohammed ya yi zargin cewa kasar Birtaniya tana yi wa Najeriya zagon-kasa a yakin da take yi da ta'addanci.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN, ya ambato Mr Lai Mohammed yana cewa matakin da Birtaniya ta dauka na bai wa wasu masu fafutukar ballewa daga kasar 'yan kungiyar IPOB mafaka "rashin mutunci ne da kuma zagon-kasa" ga Najeriya a yakin da take yi da ta'addanci.
Ya kara da cewa tuni Najeriya ta ayya na 'yan kungiyar IPOB a matsayin 'yan ta'adda don haka bai ga dalilin da zai sa Birtaniya ta nemi ba su mafaka ba.
"Idan ya tabbata cewa da gaske Birtaniya za ta bayar da mafaka ga 'yan IPOB da MASSOB da ake zargi ana musgunawa, lallai akwai matsala. Ba wai kawai an haramta IPOB a Najeriya ba ne, an kuma ayyana ta a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.
Bashin $1bn da Najeriya za ta karbo
Majalisar dattijan ƙasar ta ce ta amince wa gwamnatin tarayya da jihohi su karɓo bashin dala biliyan ɗaya da rabi kwatankwacin naira biliyan dari bakwai da hamsin da kuma yuro miliyan ɗari tara da casa'in da biyar, kimanin naira biliyan ɗari biyar da saba'in.
Ta ce ta ga buƙatar amincewa da ciyo bashin wanda tallafin annobar korona ne saboda ƙudurin gwamnatoci na farfaɗo da harkoki bayan matsin tattalin arziƙi da annobar ta jefa duniya.
'Yan Najeriya da dama suna kokawa da yawan bashin da ƙasar ke ci a ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Buhari
Daukar fansar da mazauna kauyukan Jihar Zamfara yi kan 'yan Fashi
Bayanai daga jihar Zamfara a arewacin Najeriya na cewa wasu 'yan fashin daji sun kwashi kashinsu a hannu a daren Juma'a lokacin da suke ƙoƙarin farmaki kan wasu ƙauyuka biyu da ke kusa da babban birnin jihar.
Ƴan fashin a kalla 10 ne suka mutu a cikin bata kashin da suka yi da 'yan banga a ƙauyukan Kwaya da kuma Kura da ke ƙaramar hukumar Gusau.
Wannan na zuwa ne yayin da mazauna ƙauyukan nan shida da suka kai wa farmaki a ranar Laraba ke cewa adadin wadanda suka mutu yanzu ya kai 80.
A cewar mazauna yankin 'yan fashin dajin sun gamu da gamon nasu ne a wani artabu da 'yan banga a ƙauyukan Kwaya da kuma Kura lokacin da suka yi yunkuri afka musu da tsakar daren jiya.
Wani ɗan sa kai da aka yi fafatawar da shi, ya ce turjiyar da suka nuna da kuma ɗaukin da aka kai daga maƙwabtan ƙauyuka ne suka taimaka musu suka fatattaki maharan tare da hallaka 10 daga cikinsu.
Sacewa da kashe wasu daliban Jami'ar Greenfield ta Kaduna
Ma'aikatar tsaro ta jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce yan bindiga sun kashe dalibai uku na na Jami'ar Greenfield da aka sace a Jihar.
Cikin wani sakon Twitter da Ma'aikatar ta fitar ta ruwaito Gwamnan Jihar Nasir El-Rufa'i ya yi Allah-wadai da wannan mummunan rashin imani ga rayuwar dan adam.
Ya kara da cewa dole a yaki wadannan 'yan bindiga ta ko wanne hali.
Ya kuma ce sharri ba zai taba yin nasara ba kan alheri. Ya kuma aika ta'aziyyarsa ga mutanen jihar da iyayen yaran da suka rasa yarukansu.
Kuma gwamnati za ta gaba da shaida wa mutanen jihar halin da ake ciki game da lamarin.