Shirin ba yana nufin hada husuma tsakanin ma'auratan ba ne, amma shi ne irinsa na farko da zai binciki sirrin miji ko saurayi da aka fara a Kano, arewacin Najeriya.
Dalibin Sulaiman Mohammed mai shekaru 22 wanda shi ne shugaban kamfanin karba da kai sakonni na Tall Yaro Express ya ce, a shekarar da ta gabata ne ya zauna ya yi duba kan yadda zai inganta kasuwancinsa na kai sakonnin, lokacin da wannan tunani ya zo masa a rai.
"Ina da abokai da dama da ke harkar fasahar zamani, don haka na fara tunanin lokaci irin wannan da ma'aurata za su san duk wani abu da masoyansu ko abokan zamansu ke yi, dama ce da ba kawai mutum zai iya yin abubuwa kadai ba, har ma da bude wa wasu hanyoyi, na tuntube su kuma suka nuna amincewarsu.''
"Ta hakan ne na fara aikin binciken gano ko saurayi da budurwa ko miji da mata na ha'intar juna a Kano kusan sama da wata guda kenan, kuma yanzu haka na samu kostomomi biyar da suka gamsu.''
Dalibi a fannin aikin gona ya ce ba za su fada maka cewa mijinsu na ha'intarsu dari bisa dari ba.
"Don haka abin da nake yi wa kostomomina bayan sun ba ni sunayen wuraren da masoyan ko abokan zaman nasu ke zuwa yana aiki ko kuma hutawa.
"Mu kan rika bin diddiginsa muna samar musu da bayanai game da abin da suke yi a duk lokacin da suka bukata.''
"Misali idan ka kira ka ce ga a a inda yake a yanzu, za mu fada masa cewa yana wurin cin abinci tare da abokai.
"Mu kan yi kokarin kauce wa duk wata hatsaniya, don haka ba ma cewa abokin zama ko saurayi ko budurwa na ha'intarka kai tsaye, wannan ya rage ga shi kansa mtutumin ya gano.''
Sulaiman ya ce tun bayan da ya ƙirƙiro sabuwar hanya ta wannan kasuwanci nasa mata kusan 20 ne suka kira shi suka nuna sha'awarsu na aikin binciken gano ha'incin.
"Mata kusan 20 ne suka kira ni a cikin kwanaki kadan da suka gabata suna nuna sha'awar wannan sana'ar tawa ta binciken ƙwaƙwaf, don haka wani abu ne da ke da alamar samun karɓuwa sosai.''
Matsalar da wanda ya ƙirƙiri wannan shirin ita ce bai samu lasisin amincewa daga gwamnati ba.
"A yanzu dai ban samu amincewar gwamnati ba, amma ina fata wannan abu ne da za ta amince in cigaba da yi tun da kasashen duniya da dama na barin masu aikin bincike masu zaman kansu masu rijista gudanar da aikinsu.''
Walida Sani ta shaida wa BBC cewa ta biya Sulaiman don ya bincika mata saurayinta lokacin da ta fara zargin yana ha'intar ta, kuma ta ji dadin yin hakan.
"Lokacin da na fara zargin saurayina na ha'intata, na samu labarin abin da Sulaiman ke yi, na yi magana da shi na kuma biya shi don ya bincike ko me saurayina ke ciki, kudin babu tsada kuma duka aikin ya faru a tsakanin kwanaki uku.''
"Bayan binciken ne hankali na ya kwanta cewa saurayina ba ya ha'inta ta, amma saboda gaba zan cigaba da amfani da wannan hanya a duk lokacin da bukatar ta taso.''
Gwamnatin jihar Kano a karkashin hukumar Hisbah da ke da karfin fada-a-ji a jihar ta ce abinda Sulaiman ke yi ba tare da amincewar hukuma ba ba daidai ba ne.
Kakakin hukumar ta Hisbah Lawal Fagge ya bayyana cewa hukumar ba za ta amince da duk wani abu da ya saba ƙa'idar addinin Musulunci ba.
Kuma muddin mutane suka rubuto musu game da ayyukan Sulaiman za su gudanar da bincike in ji Fagge.''
"Muddin mutanen da ba su gamasu da irin ayyukan da yake yi ba, suna iya rubuto mana don gudanar da bincike, amma a fili take cewa hukumar Hisbah ba za ta amince da duk wani abu da addinin Musulunci bai yarda da shi ba.''
Sulaiman ya ce yana da ma'aikata huɗu a yanzu, amma yana fatan zai ƙara wasu da zarar kasuwancin nasa ya ƙara bunƙasa.