Neymar ya ce wannan kakar ta bana ita ce yake cike da farin ciki a Paris St Germain, duk da rade-radin da ake kan makomarsa a Faransa.
Har yanzu dan kasar Brazil, mai shekara 29 bai saka hannu ba kan tsawaita zamansa a PSG, bayan da yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar badi.
An ta alakanta shi da cewar zai koma tsohuwar kungiyarsa Barcelona wadda ya bari ya koma PSG kan fam miliyan 200 a shekarar 2017 a matakin mafi tsada a duniya.
Neymar ya ce ''Wannan kakar ta bana PSG ta kara bunkasa, kuma muna sa kwazo don kara daga darajar kungiyar.''
''Muna matukar son lashe Champions League.''
Ranar Laraba ne Paris St Germain za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan farko na daf da karshe a Champions League.
Neymar ya ci kwallo shida a karawa bakwai a Champions League a bana, wanda ya zura kwallo 14 jumulla a wasa 24 a dukkan fafatawa.
PSG wadda ta nada Mauricio Pochettino kocinta a cikin Janairu tana ta biyu a kan teburin Ligue 1 da tazarar maki daya tsakaninta da Lille.