BBC Hausa of Thursday, 3 June 2021

Source: BBC

Wasika daga Afirka: Damfarar masu kwadayin samun dukiya cikin sauri a kasar Kenya

Damfarar kudaden intanet na kama wuta a Kenya Damfarar kudaden intanet na kama wuta a Kenya

A irin jeri wasikunmu daga 'yan jaridun Afirka, wani dan jaridar kasar Kenya Waihiga Mwaura ya yi rubutu game da masu damfarar kudaden intanet, da suka hada da wadanda aka yi kasuwancinsu ta hanyar amfani da sunansa wajen janyo hankalin masu zuba jari.

Wani likita da ban san shi ba ya kira ni ta waya, yana tambaya ta ko na yi hira da wani hamshakin attajirin kasar Kenya game da sabon kudin intanet na Bitcoin a wani shafin intanet da ba a tantance sahihancinsa ba.

Na yi wata ajiyar zuciya cike da damuwa saboda na san cewa ya fada tarkon masu zamba ta shafin intanet da aka shafe shekaru biyu ana yi inda wasu suke zargin cewa ni da wani attajiri mun amince da shafin kasuwancin kudaden intanet.

Duk da irin kokarin da na yi wajen yin gargadi ga 'yan kasar Kenya game da masu aikata zamba ta hanyar amfani da shafina na sada zumunta, da alamu wadannan bata-gari sun ci gaba da sauya adireshin shafin intanet da kuma tsarin yadda suke gudanar da zambar don kai wa ga 'yan kasar ta Kenya da tsautsayi ka iya fadawa a kansu, da ke fatan watan wata rana komai zai tafi musu daidai.

A wani abu da ya kasance kwadayin shiga kasada - da neman kudi a saukake - da dama sun fada tarkon tsarin zuba jari na na ban-biyar-in-ba-ka-goma wato Ponzi Scheme wanda da farko ya kasancewa kamar abin nema ya samu ne.

An kama wata Ba'amurkiya

Zamba ta baya-bayan nan da aka bankado a kasar Kenya ita ce ta hanyar manahajar da ake kira Amazon Web Worker Africa, wacce ke ikirarin cewa wani bangare ne na kamfanin cinikayyar kayayyakin nan na Amazon Inc, kuma za a iya shiga ta cikin wayar salula da kuma manahajar intanet.

Amma kuma ba shi da wata alaka da kamfanin cinikayyar kayayyakin mafi girma a duniya.

Makonni kadan da suka gabata, masu zuba jari a kamfanin na Amazon Web Worker sun wayi gari da ganin an goge manhajar daga babbar manhajar sauke manhajoj ta Google Play Store ba tare da wata sanarwa a hukumance ba da kuma jarin da suka zuba, wanda wasunsu sun kai dubban daloli, yanzu babu damar su san abin da ake ciki.

Bukatun sun kasance masu sauki, za a biya ka kudi kan sanar da sauran mutane game da manahajar.

Za a yi maka alkawarin wani kaso na ladan abin da ka yi yayin da jarin da ka zuba na farko ke ci gaba da kasancewa babu wata matsala.

Bayan bacewar manhajar, daruruwan 'yan kasar Kenya sun yi ta tururuwar shiga shafukan sada zumunta daban-daban don nuna damuwarsu, yayin da wasu ke nuna matukar bakin cikinsu cewa abokansu da 'yan uwansu ne suka gabatar musu da "damar zuba jarin."

Labari mai dadin ji shi ne cewa mahukuntan kasar Kenya sun sanar da kama wata Ba'amurkiya mai shekaru 50 da ake zargi da hannu a kan abin da ya yi kaurin suna "Zambar Amazon Web Worker".



'Yan sanda sun ce ana zarginta da kasancewa cikin gungun masu zambar kuma za a hukunta ta kan halarta kudin haram da kuma zamba ta shafin intanet.

Kama ta - da aka yi bayan saukarta a babban filin saukar jiragen sama na birnin Nairobo - ya karfafa wa wasu da suka zuba jarin gwuiwar cewa za a dawo musu da kudadensu.

Damfarar zuba jari a kasar Kenya yanzu ta zama ruwan dare kuma mai yiwuwa za a iya danganta hakan da rashin aikin yi.

Binciken da hukumar kididdiga ta kasar Kenya ta yi kafin barkewar annobar korona ya nuna cewa kashi 40 bisa dari na matasan kasar Kenya sun rasa aikin yi a cikin watan Fabrairun shekarar 2020.

Kana a yayin da ake cikin karo na uku na annobar, halin da ake ciki game da rashin aikin yi ya kara tabarbarewa, duk da cewa ba a riga an fitar da sabon sakamakon binciken ba.

Zambace-zambacen kan zo ta fuskoki da sigogi daban-daban - daga hanyar samun kudade cikin sauri, da zuba jari a fannin ayyukan gona na lokaci guda, da na garabasar samun gidaje, sai na tsarin cinikayyar kudaden kasashen waje ta shafin intanet, har ma da na wasan dara, da kuma tsare-tsaren hakar ma'adinan kudaden intanet.

Kasuwar hada-hadar kudaden intanet cike take takaddama da tsare-tsare biyu na Ponzi kan kudin intanet na Bitcon a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Menene tsarin ban-biyar-in-ba-ka-goma?

  • Akan bai wa masu zuba jari na farko lada mai yawa kan zuba jarin da suka yi, amma kuma suna bukatar kawo wasu masu zuba jarin a kan tsarin don ci gaba da samun ladan


  • Ana janyo hankalin karin masu zuba jari su shiga tsarin, amma kuma riba kadan suke samu daga jarin da suka zuba, saboda akan yi amfani da jarin da suka zuba wajen biyan wanda ya kawo su da kuma kara wa kamfanin karfi. Don haka suna bukatar karin masu zuba jarin ne don kara yawan kudaden shiga


  • Tsarin yakan durkushe a lokacin da yawan masu zuba jarin ya ragu kana kudaden shigar suka yi kasa.


  • A daya daga cikin damfarar kudaden na intanet, an bayyana cewa masu zuba jarin akasari 'yan kasar Kenya sun yi asarar fiye da dala miliyan 25 kuma ba su samu farfadowa ba.

    Na tattauna da wani mai zuba jari da ya yi asarar kusan $30,000 ga wani tsarin hada-hadar kudaden intanet na Afirka, kuma abin mamaki ya bayyana min cewa kwadayin shiga kasada zai sa ya sake gwada sa'arsa muddin bai samu yadda yake so ba.

    Muddin dai mutane na da irin wannan tunani, to kuwa lallai babu tantama cewa za su ci gaba da asarar kudadensu.