Ranar Laraba hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa za ta fayyace ko ya kamata ta mai da wasan karshe na Champions League zuwa Wembley.
Tun farko an tsayar da ranar 29 ga watan Mayu, domin buga wasan karshe a Istanbul, amma dokar shiga kasa tsakanin kasashen don hana yada cutar korona za ta kai tsaiko.
Ranar Litinin Uefa za ta yi zama da gwamnatin Burtaniya da mahukuntan kwallon kafar Ingila kan wurin da ya kamata a yi wasan karshen a gasar Zakarun Turai.
Kungiyar Chelsea da ta Manchester City ne daga Ingila za su buga wasan karshe a gasar ta Champions League ta bana.
Tuni aka gargadi magoya baya daga Ingila cewar ba za a bari su shiga Turkiya ba, sakamakon dokar hana yada cutar korona tsakanin kasa da kasa.
Hakan ne ya sa hukumar kwallon kafa ta Ingila ta bukaci a yi wasan a Wembley tun da dai karawar ta 'yan kasa daya ce.
Dokar Burtaniya ta tanadi duk wanda ya ziyarci kasar dake da hadarin kamuwa da cutar korona, idan zai koma gida sai ya killace kansa a otal din da gwamnati ta amince da shi na kwana 10.
Wannan killacewar za ta shafi 'yan wasan da za su buga gasar cin kofin nahiyar Turai da ya kamata a fara daga 11 ga watan Yuni.
Tun farko Uefa ta tsara bai wa magoya bayan kungiyoyin biyu tikitin kallon wasan karshen 4,000 kowacce a fafatawar da aka tsara yi a Istanbul.