BBC Hausa of Sunday, 30 May 2021

Source: BBC

Yadda China ke saka wa Musulmai na'urar gane tunani

China na saka wa Musulmai na'urar gane tunani, inji masana China na saka wa Musulmai na'urar gane tunani, inji masana

A tsarin sarrafa na'urar daukar hoto ta kyamara da ke aiki da kirkirarriyar basira (AI) da ke gano al'amura, tare da bayyana yanayin sosuwar zuciya an gwada ta a kan 'yan Kabilar Uyghurs da ke yankin Xianjiang, kamar yadda BBC ya bayyana.

Wani Injiyan massarafar na'urar kwamfuta ya yi ikirarin kafa irin wannan tsarin na'urar a ofishin 'yan sandan da ke wannan Lardin.

Shi kuwa wani mai fafutikar hakkokin al'umma, wanda aka nuna wa hujja aikin massarafar, ya bayyanata a matsayin al'amari mai sanya kaduwa.

Ofishin Jakadancin Sin da ke Landan bai yi wani bayani a kan lamarin ba, wanda ke da alaka ta kaitsaye, amma ya yi nuni da cewa hakkokin siyasa da na zaman tare a daukacin kabilu ana tabbatar da su.

Yanki Xianjiang mazaunin kabilar da yawan al'ummarta ya kai miliyan 12 'yan Uygurs, wadanda mafi yawansu Musulmi ne.

Ana sa'ido kan mazaunan wannan Lardi. Wannan yanki ne da ke cike da takaddamar "cibiyoyin sake ilimantarwa," wadanda kungiyoyin fafutikar hakkokin al'umma ke yi wa lakabin sansanonin garkame mutane, inda aka kiyasta a kalla ana tsare da mutanen da yawansu ya kai miliyan guda.

Gwamnatin Beijing ta jajirce kan cewa, sa'ido da lura da al'umma ya zama dole a yankin saboda a cewarta, 'yan aware, wadanda ke son kafa kasarsu sun hallaka daruruwan mutane ta hanyar farmakin ta'addanci.

Injiniyan massafar kwamfutar ya amince ya tattauna da shirin BBC na bayyana al'amura karara, tare da yarjejeniyar alkawarin ba za a bayyana mutumin da aka tattauna da shi ba, saboda yana tsoron kare rayuwarsa.

Kuma Kamfanin da yake yi wa aiki ma ba za a bayyana ba.

Ko da yake dai, ya nuna wa shirin bayyana al'amura karara na 'Panaroma' hotuna biyar na mutanen da ake tsare da su, wadanda ya yi ikirarin cewa an lika musu ma'aunin gwajin kirkirar basira ta AI.

"Gwamnatin kasar Sin na amfani da mutanen Uyghurs don yin gwaje-gwaje daban-daban, tamkar dai yadda ake amfani da beraye a dakunan binciken kimiyya," inji shi.

Ya bayyana irin rawar da ya taka wajen kafa wadannan na'urorin kyamara a ofisoshin 'yan sandan da ke Lardin.

"Mun makala na'urar kyamarar auna sosuwar zuciya da nisan mita 3 daga mutumin da za a gwada. Ita ma kwakankwacin na'urar gano karya ce, kodayake wannan fasahar kirkirar ta kai makura."

Ya ce jami'an na amfani da "kujerun takurewa," wadanda aka kakkafa su da yawa a ofisoshin 'yan sanda da ke kasar Sin.

"Wuyan hannunka zai kasance a daure, tamkar yadda ake yi wa idon kafa."

Ya gabatar da hujjoji kan yadda aka tsara dabarun amfani da kirkirar basirar AI wajen gano sauye-sauyen yanayin fuska da kofofin fata.

Kamar yadda ikirarinsa ya nuna, masarafar na fitar da jaddawalin alamar kurin 'Pie Chart', mai barin ja da ke nuni da rashin jin dadi ko dugunzumar damuwar tunani.

A cewarsa, manufar wannan massarafar, ita ce, yanke wa mutum hukunci ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Ofishin jakadancin kasar Sin da ke birnin Landan, bai bayar da wani bayanin amsar tambayoyin da aka bijiro da su game massafar na'urar gano darsuwar zukata ba, amma ya bayyana cewa:

"Akwai tabbacin samun hakkokin siyasa da hada-hadar tattalin arziki da walwalar zamantakewa da 'yancin yin addini a tsakanin daukacin kabilun da ke yankin Xianjin."

Mutane na zaman tare cikin lumana ba tare da la'akari da kabilar da suka fito daga ciki ba. Kuma suna samun rayuwar aminci ba tare da wata takurar rashin 'yancin ba."

Dalili kan hakan an nuna wa Sophie Richardson Darakta Sa'ido kan 'yancin dan Adam a kasar Sin,

"Na'urar na da matukar tayar da hankali. Ba wai kawai an kaskantar da mutane ne a jaddawalin kurin 'Pie chart" ba, wato mutanen na cikin wani irin mawuyacin halin tursasawa, lamarin da ke haifar da matukar damuwa, kuma shi ake dauka alamar tabbatar da zargin aikata laifi, sannan ina jin cewa wannan babbar matsala ce. Ita dai dabi'ar tabbatar da zargin aikata laifi ce.

A cewar Darren Byler na Jami'ar Colarado, akai-akai 'yan kabilar Uygurs na bayar da samfurin kwayoyin halittarsu ga jami'an hukumar yankin, inda akan gudanar da gwajin na'urar kwamfutar binciken hotunan sassan jiki.

Kuma dole a sauke su a manhajar massafarar tarhon aikewa da sakonni ga gwamnati, inda ake tattara bayanan da suka hada da mutanen da ke mu'amala da su a wayarsa/ta, tare da sakonnin tes-tes da ya/ta aike a su.

"A halin yanzu rayuwar Uyghur ta ta'allaka ne wajen tattara bayanai," in ji shi.

"Kowa na sane da cewa manyan wayoyin hannu na alfarma dole ne mutum ya rike su, kuma kin aikata hakan na iya haifar wa mutum dauri a kurkuku, domin sun san cewa ana bibiyarka/ki a ko'ina.

Sannan suna jin cewa babu yadda mutum zai tsira," inji shi.

Mafi yawan bayanan da ake tattarawa ana alkinta su ne a cikin na'urar kwamfutar da aka yi wa lakabin dandamalin cure hadakar ayyuka, al'amarin da masu fafutikar hakkokin dan Adam ke ganin su ake amfani da su wajen dabi'ar tabbatar da zargin aikata laifi.

"Tsarin dai na tattara bayanai ne game da al'amura da dama mabambanta a rukunin dabi'un da doka ke iya tabbatar da su, wadanda suka hada da gano cewa, ko mutane na fita waje ta kofar baya, maimakon ta kofar gaba, ko kuwa suna zuba wa motar da ba ta su mai ba," a cewar Richardson.

"A halin yanzu dai mahukunta sun saya na'urar nazarin hotunan kai-kawon mutane ta 'QR' a gaban kofar gidajen mutane, ta yadda cikin sauki za a iya gano mutumin da yake wurin da wanda ma baya nan." Manuniyar shaguben Orwell?

An dai dade ana ta tafka takaddamar muhawara kan cewa ko kamfanonin fasahar kirkirar kasar Sin ta kama kafar binciken kasar Amurka na IPVM, wadanda suka yi ikirarin tabbatar da hujjar wannan aiki.