BBC Hausa of Saturday, 10 April 2021

Source: BBC

Yadda Yarima Philip ya zama garkuwa da gatan Sarauniya

Yarima Philip mijin Sarauniyar Ingila Yarima Philip mijin Sarauniyar Ingila

Ga shi sirikin sarki, mijin sarauniya kuma baban sarkin gobe, amma duk da haka, Maji Dadin Edinburgh ba shi da wani aiki a hukumance.

Aurensa da sarauniya ya kara masa martaba da samar masa mafaka irin ta siyasa da kwanciyar hankali da kuma nutsuwa, kamar yadda auren ya tabbatar da kasancewarsa cikin hidimtawa matarsa, yana biye da ita, duk inda ta sa kafa ta dauke, nan zai jefa tasa.

An taba tambayarsa dangane da gudummawarsa ga Burtaniya, sai ya kada baki cikin salonsa na ba da amsa kai-tsaye ya ce 'na yi iya kokarina. Wasu mutanen sun yi sam-barka, yayin da wasu kuma sukan yi akasin hakan. Yaya mutum zai yi? Wannan wani salo ne na rayuwata wanda ba zan iya sauyawa ba. Wani abu ne da ba yadda mutum ya iya da shi.

Yin waiwaye a kan kuruciyarsa zai taimaka wajen fahimtar wane ne shi. Philip shi ne da daya tilo ga Yarima Andrew na kasar Girika da gimbiya Alice ta Battenberg.

Mahaifinsa ya kasance dan gidan sarautar Denmark sannan kuma yana da alaka da sarakunan Greece da Denmark da Prussia da kuma sarakunan Rasha. Duk kuwa da wannan kyakkyawar nasaba, Philip yana bayyana kansa a matsayin dan gudun hijira.

An kori dangin su Philip daga tsibirin Girika da ke Corfu watanni goma sha takwas bayan haihuwarsa, a yayin da Girika take yaki da Turkiya. Wani jirgin rowan yakin Birtaniya ne ya tseratar da su, inda aka saka Philip a lokacin yana yaro a cikin wani dan gadon yara.

Philip ya fuskanci matsananciyar rayuwa a lokacin yarintarsa. Iyayensa sun rabu, inda mahaifinsa (manemin mata) ya koma Monte Carlo.

Mahaifiyarsa kuwa, ita ma ta gamu da ibtila'in rayuwa, bayan da ta bayyana cewa ta zama sayyada. Daga baya sai ta koma harkar addini kuma ta kebe kanta.

Matsanancin Lokaci

Philip bai sa mahaifiyarsa a idonsa ba har tsawon shekara bakwai. 'Yan'uwansa da kuma makarantun kwana da ya yi su ne suka maye masa gurbin iyayen nasa.

Makarantarsu ta Gordonstoun ta fi mayar da hankali wajen nuna wa mutum yadda zai tsaya da kafarsa ta hanyar jajircewa da kuma dogaro da kai.

Daga baya, Yarima ya dinga yin maganganu a bainar jama'a, inda ya bayyana yadda rayuwarsa ta kasance. Amma in ba a cikin mutane ba, ba sosai ka fiye jin kansa ba.

Duk kuwa da matsananciyar rayuwar da ya fuskanta a baya, amma sai ga shi ya kasance mutum mai dogaro da kai, mai damuwa da rayuwarsa wanda da wuya ka gane wani abu da yake damunsa.

Makarantu hudu da ya halatta a shekaru goma sun sa shi a cikin bulayin gano wane ne shi, kafin haduwa da gimbiya Elizabeth wadda ita ce ta sauya rayuwarsa.

Himmatuwa

Sun fara haduwa ne a makarantar Royal Nabal College da ke Dartmouth, a shekarar 1939.

Gimbiya Elithabeth ta fada cikin tarkon kaunar matashin sojan da ke karbar horo, tun a lokacin tana shekara 13, inda shi kuma yake dan shekara 18, yayin da yake shakatawa a wasan Tenis.

A yayin yakin duniya na biyu ne ta ajiye wani hotonsa da dan gemunusa, yana sanye da kayan sarki na sojojin ruwa, a kan teburin dakinta na kwalliya.

Gimbiya Elithebeth ta himmatu sosai, kuma ta kudiri aniyar saka kafar wando daya da duk wasu ma'aikatan fada da suke sukar soyayyarsu kuma suke kallon masoyin nata a matsayin wani talakan yarima daga wata kasar daban.

A lokacin da ya bayyana a gidan sarauta a lokacin yakin duniya, duk sun firgita, tun da kuma ga shi bai taba zuwa Eton ba.

Muhimmin lokaci

An daura musu aure a shekarar 1947 wanda ya yi daidai da lokacin da aka fuskanci tsanani bayan shekarun da aka sha fama da duhu dukununu ga kuma karancin abinci.

Wani abokin ma'auratan ya bayyanawa BBC cewa 'yanayin ya kasance tamkar fitowa ne daga wani surkukin duhu zuwa haske'

Ma'auratan sun sha kyaututtuka, wadanda suka hada da wani leshi sakar hannu daga Mahatma Ganddhi wanda sarauniya Mary, kakar gimbiyar, ba ta ma gane yanayinsa ba.

Shekarun farko bayan auren, sun kasance masu muhimmanci sosai a wajen Yarima. Kwarewarsa a sojan ruwa ta kara bunkasa, musamman ma lokacin da yake a Malta.

Mutum ne haziki wanda yake iya kokarinsa wajen aiwatar da abin da yake so, to amma zamansa a yankin Mediterranean na tsawon shekara biyu ne rak.

Rashin lafiyar surikinsa ta sa dole ayyuka suka fara dawo wa kan matarsa. A lokacin da suka bar Malta a 1951, innar Philip ta bayyana cewa: "Dawowarsu tamkar mayar da kwarya gurbinta ne".

Bayan shekara daya sai sarki ya rasu. Wani abokin yariman ya taba cewa, a wannan ranar da fahimci cewa matarsa ta zama sarauniya, sai ya ji tamkar an dora masa Dala da Goron Dutse.

Sarauniya ta rungumi kaddarar da ta fado mata, duk da cewa mutuwar babanta ta shammace ta, to amma Yarima Philip ya kasance a cikin wani irin yanayi na daban. Dole ya bar aikinsa da yake matukar so.

Ya taba bayyana wa wani dan jarida cewa "Ba burina ba ne zama shugaban kwamitin ba da shawarwari na gidan sarauta. An dai sa ni ne kawai.

A gaskiya na fi so na ci gaba da kasancewa a aikina na sojan ruwa".

Duk da kasancewarsa na mijin sarauniya, bai sami wata sarauta ba. Ya zamanto mutum na farko da ya yi mata mubaya'a a wajen nadin sarautar.

Philip ya taba ambatawa cewa "A hukumance, ba ni da wani mukami, ba ma a san da nib a." Bai sami ko da mukamin yarima mijin sarauniya ba; 'ya'yansa ma ba sa amfani da sunansa, wato Mountbatten; sannan kuma ya yi ta gwagwarmaya a shekarar 1950.

Abubuwan tunawa

Tamkar ragowar 'ya'yan sarauta, Philip ya yi kokarin neman irin gudummawar da ya kamata ya bayar. Abu ne mai sauki a ga abubuwa iri-iri birjik, idan aka zo kimanta gudummawarsa.

Irin subul-da-bakan da Yarima ya dinga yi, abin a tuna ne.

Misali, ya taba jan kunnen wasu daliban Burtaniya a birnin Sin cewa za su iya zamantowa masu kananan idanu, sannan kuma ya taba tambayar wani mutumin karkara da cewa: " Wai shin har yanzu kuna jifan junanku da mashi?"

To amma abokansa suna ikirarin cewa abubuwan da ya bari, sun fi gaban haka. Sun siffanta shi da wani mutum mai son cigaban muhalli da kimiyya da masana'antu da kuma al'amuran samari, musamman a karkashin shirinsa na kyaututtukan Yariman Edinburgh.

Wannan ya sa wasu sun fara sauya tunani a game da shi, kamar yadda a da akan sami masu zarginsa, kamar yadda wani jami'in gwamnati ya zarge shi da yunkurin samar da kwatankwacin samarin Hitler a Birtaniya.

Garkuwata

Masoyan Yarima sun tabbatar da cewa, babbar gudummawarsa ita ce irin cikakken goyan baya da ya ba wa sarauniya.

Irin rawar da ya taka a rayuwar sarauniya, watakil ya kasance abin da masana tarihi za su fi mai da hankali a kai.

A duk lokacin da ma'auratan suke tare, yakan yi kokarin samar da yanayi mai kyau da kuma yunkurin daga yara sama domin su kawo gaisuwa ga matar tasa.

A wasu kalamai da ba kasafai aka fiye jin su daga gare ta ba, dangane da alakarsu, Sarauniya ta bayyana Yarima a matsayin garkuwarta a tsawon rayuwarta.

Tabbas, wadanda suka san su tare za su aminta da wadannan kalamai.

Wani tsohon hadimi ya bayyana Yarima Philip da cewa, shi ne mutum daya tilo da yake yi mu'amalantarta a matsayin abokin rayuwarta. Ita ke rike da sarautar amma shi ke rike da rayuwarta.

Wannan wata alaka ce tsakanin wata mace mai matukar kulawa da kuma mutum mara kwana-kwana, tabbas wannan alakar tasu ta yi karko, domin hatta auratayyar 'ya'yansu guda uku daga cikin hudu sai da aka sami matsala.

Rashin jituwa

Philip ya gaya wa wasu taron masu sauraren sa cewa, juriya ita ce sinadarin zaman aure. Sai kuma ya bayyana matarsa da cewa tana da wannan arzikin wannan sinadarin.

Yarima Philip yana nan a lokacin da hatsaniya ta kacamewa fadar Windsor a shekarun 1980 da kuma 1990.

A wasu lokutan sukan samu 'yan matsaloli da babban dansa, to amma daga baya alakar ta gyaru.

Wata rana ya taba magana dangane da yarima Charles, inda ya bayyana shi da cewa:

"Shi mutum ne mai son soyayya, ni kuma ba na gewaye-gewaye, saboda ni ba na ganin abubuwa a yadda gwanayen soyayya suke ganin su, don haka ni ban damu ba.

A satin nan mafi tarnaki a duk tsawon mulkin sarauniya, wato bayan mutuwar Diana, gimbiyar Wales, Yarima Philip ya kasance tare da matarsa lokacin da ta dawo London bayan ta sha sukar cewa tana baya-baya da lamarin, a wannan lokacin kuma suna tare da jikokinsa a sa'ilin da suke biye da akwatin gawar mahaifiyarsu.

Bai ce ko uffan ba, a lokacin da Mohamed Al Fayed yake ta nanata zargin cewa Yariman ne ya yi sanadiyyar kashe gimbiya Diana.

Tarin ayyuka

Bayan sun nemi ya kare kansa, an fito da irin wasikun da ya dinga tura wa matar dan nasa bainar jama'a.

Sun kalubalanci abin da ya yi, domin sun nuna shi a matsayin siriki amma yana kokarin gyaran auren gimbiya, bayan auren ya mutu.

A watan Yuni na shekarar 2011 ne ya cika shekara 90 da haihuwa, inda a fili ta bayyana baro-baro cewa shekarunsa fa sun ja.

Ya bayyana wa BBC cewa shekaru sun cim masa, ya fara tattara komatsansa, don haka zai rage yawan aikace-aikace, dalili kuwa a fadarsa shi ne,: "kamata ya yi in janye jikina kafin karfina ya kare".

Amma sai ga shi bayan shekara daya, sun yi tafiye-tafiye tare da sarauniya a lokacin da take bikin cikarta shekara sittin a kan karagar mulki. Sai bayan kusan shekaru shida tukuna ya fara nuna alamun janyewa daga ayyukan masarauta.

Lallai mutuwar yarima Philip ya haifar wa da sarauniya kadaici, kasancewar shi ne ke taimaka mata wajen ci gaba da gudanar da masarautar Birtaniya.

Yarima Philip ne kadai, sai kuma marigayiya sarauniya Elizabeth, wato mahaifiyar sarauniya da kuma 'yar'uwarta gimbiya Margaret su ne suka fi kowa fahimtar matsalolin rayuwarta. Don haka, sarauniya za ta ci gaba da mulkarmu ciki bakin ciki da kadaici.

Yayin da aka tambaye shi game da wane irin sakon tunawa da mamaci yake so ya bari, domin an san mutum ne shi da ya san kan masarautar, amma sai ya kada baki ya ce: "ni hakan bai dame ni, domin zan mutu kafin wannan lokaci".

Dukkanin hotuna suna da hakkin mallaka