BBC Hausa of Wednesday, 5 May 2021

Source: BBC

Yadda ƙarancin ungozoma ke sanadin rayukan miliyoyin mata da jarirai a duniya

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce duniya a yanzu na fama da ƙarancin ungozoma dubu 900 Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce duniya a yanzu na fama da ƙarancin ungozoma dubu 900

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce miliyoyin mata da jarirai ne ke mutuwa, yayin da wasu miliyoyin ke fama da rashin lafiya ko kuma rauni saboda ba a martabawa ko fifita bukatun mata masu juna biyu da kuma bai wa ungozomomi kwarewa.

Ta ce duniya a yanzu na fama da ƙarancin ungozoma dubu 900, abin da ke wakiltar kashi ɗaya cikin uku na ungozomar da ake buƙata a duniya.

A cewarta annobar korona ta ta'azzara waɗannan matsaloli, saboda ta dusashen buƙatun lafiya na mata da jarirai.

Wannan wani ɓangare ne na muhimman batutuwan da ke ƙunshe cikin rahoton Halin da aikin Ungozoma ke ciki a shekara ta 2021 a duniya na Asusun kula da Yawan jama'a na Majalisar Ɗinkin Duniya da Hukumar Lafiya ta Duniya da kungiyar ungozomomi da ya yi nazari akan kasashe 194.

Karancin ungozomomi na kawo nakasu a kokarin da ake yi wajan rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da jarirai.

Wani rahoto da aka wallafa a mujallar Lancet ya nuna cewa idan aka inganta fanin nan da shekarar 2035 za a iya samun raguwa a yawan mace macen mata masu juna biyu da kashi 67, da kuma na jarirai da kashi 64.

Rahoton ya yi kiyasin cewa rayuka sama da miliyan hudu za a ceto a kowace shekara.

Sai dai duk da damuwar da aka nuna a rahoton da aka fitar a shekarar 2014, wanda ya bada shawara kan yadda za a shawo kan matsalar kawo yanzu matsalar ba ta sauya zani ba a cikin shekaru takwas da suka gabata.

Haka kuma rahoton na bana ya ce cigaban da za a samu zai kai shekarar 2030 kuma shi ma ba wani abun a zo a gani bane