Wasu iyalai a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar sun fada cikin makoki bayan gobara ta kashe 'ya'yansu fiye da ashirin da yammacin Talata.
Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe hudu na yammaci a makarantar firamare da ke unguwar Pays Bas a birnin Yamai, inda azuzuwa 28 da aka yi su da zana suka kone kurmus tare da halaka dalibai kananan yara akalla 20.
Walikiyar BBC a Yamai, Tchima Illa Issoufou, ya rawaito cewa gobarar ta fara tashi ne daga kofar shiga makarantar, mai dalibai akalla 800.
Ya zuwa yanzu ba a san musabbabin gobarar ba.
Sai dai hukumar kashe gobara ta kasar ta ce azuzuwan suna manne da juna lamarin da ya sa gobarar ta munana, yaran kuma suka makale babu ta inda za su fita.
Shugaban hukumar kwana-kwana na birnin Yamai ya ce jami'ansa sun isa makarantar a kan lokaci, an kuma yi nasarar kashe wutar.
Sai dai ya ce an kafa azuzuwan ne a kusa da rariya, kuma iska ta yi ta kadawa wadda ita ma ta kara rura wutar.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato jami'in kungiyar malamai Mounkaila Halidou na cewa: "Rashin kofar fitar gaggawa ya sa dalibai da dama sun makale sannan ya tilasta wa wasu haura katanga. Wadanda suka mutu yawanci kananan yara ne da ke matakin raino."
Firaiministan Ouhoumoudou Mahamadou da ministan ilimin kananan makarantu da gwamnan birnin Yamai sun kai ziyara makarantar, tare da yin jaje da ta'aziyya ga iyayen yaran da suka rasu.