Wasu ɗalibai a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce sun faɗa cikin rashin tabbas game da makomarsu sakamakon matakin gwamnatin jihar na ƙin biya musu kuɗin jarrabawa.
Ɗaliban, wadanda suka rubuta jarrabawar karshe ta makarantun koyar da fasaha, wato NABTEB da kuma takwarorinsu da suka yi jarrabawar kammala sakandaren Arabiyya, NBAIS, sun yi zargin cewa hukumomin da ke gudanar da jarrabawar sun ƙi ba su sakamakonsu saboda gwamnatin Kano ba ta biya musu kuɗaɗen jarrabawar ba.
Fiye da ɗaliban sakandaren fasaha dubu goma da na ɓangaren Arabiyya sama da dubu 13 da ke jihar ta Kano ne ba su san makomar karatunsu ba sakamakon rashin biyan kuɗin jarrabawar tasu.
Wasu daga cikin ɗaliban sun shaida wa BBC cewa tun watanni biyar da suka wuce ya kamata a ba su sakamakon jarrabawar amma hakan ya gagara saboda gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙi biya musu kuɗin jarrabawar.
"Gaskiya ga shi nan na yi karatu amma ban san makomata ba, na yi JAMB ga shi har shekara tana neman ta zagayo za ta lalace ban san a inda nake ba," a cewar wata ɗaliba da ke son yin karatun lauya amma ba a ba ta sakamakon jarrabawarta ba.
Kazalika wani ɗalibin Kwalejin Fasaha a Kano ya shaida mana cewa rashin abin hannun ya sa bai biya wa kansa kuɗin jarrabawar NABTEB din da ya rubuta ba, ba don haka ba da ba zai jira gwamnati ta biya masa ba.
A cewarsa: "Mun yi jarrabawar NABTEB kuma ga shi sakamakonta har yanzu bai fito ba. Mun je mun tuntuɓi malaman makaranta sun ce ba huruminsu ba ne na gwamnati ne."
Sai dai ma'aikatar Ilimi ta Kano ta ce ta damu da halin da ɗaliban ke ciki, tana mai ƙarawa da cewa tana tattauna wa da hukumomin jarrabawar NABTEB da NBIAS domin yin sulhu ta yadda za su fitar da sakamakon jarrabawar ɗaliban.
Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Sanusi Sai'd Kiru, ya shaida wa wakilinmu cewa "Nan ba da daɗewa ba za a biya wannan kuɗi kuma ita kanta hukumar mun fara magana da su, akwai yarjejeniya tsakaninmu."
Ya ce kuɗin wani bashi ne da hukumomin jarrabawar suke bin gwamnatin Kano a shekarar 2018 da 2020 yana mai rarrashin ɗaliban da su kwantar da hankalinsu.
Ko a kwanakin baya sai da aka kai ruwa rana da gwamantin Kano kafin ta biya wani kaso na kuɗin jarrabawar ɗaliban jihar na NECO.
Hakazalika wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin ta Kano ta ce za ta ciyo bashin kusan naira biliyan tara domin gina gada mai hawa uku, saboda a cewarta yin hakan zai rage cinkoson da ake yawan samu a hanyar.
Sai dai wasu daga cikin ƴan jihar, ciki har da tsohon Gwamna Rabi'u Kwankwaso, sun soki matakin suna masu bai wa gwamnati shawara ta mayar da hankali wajen bayar da ilimi da bunƙasa harkokin lafiya.