BBC Hausa of Monday, 12 April 2021

Source: BBC

Yadda hankalin manoman Koko a Ghana ya koma kan cakulat

Ghana a halin yanzu tana sarrafa kusan kashi 30% na koko Ghana a halin yanzu tana sarrafa kusan kashi 30% na koko

Akwai kuɗi da yawa a kasuwancin cakulat amma masu noman koko abin da suke samu bai taka kara ya karya ba.

Wani hasashe ya nuna cewa dala biliyan biyu kawai Ghana ta samu duk da kasancewarta ta biyu da ta fi noman koko a duniya, saɓanin kuɗaɗen da kamfanonin cakulat ke samu.

Wannan tsohon tsari ne a ƙasashen Afirka da dama inda har yanzu tattalin arzikin ke daidaita ta hanyar alaƙar mulkin mallaka inda suke fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje don sarrafa su.

Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo, a wani jawabi da ya gabatar a Switzerland a bara ya ce "ba wani ci gaba da mutanen Ghana za su samu" idan aka ci gaba da tafiya haka.

Ghana a halin yanzu tana sarrafa kusan kashi 30% na koko, amma duk da tsare-tsaren bunƙasar masana'antun cakulan na cikin gida har yanzu akwai ƙalubale.

Manomin koko Nana Aduna II - basarake, wanda ya gaji gonarsa mai girman eka 80 shekaru 20 da suka gabata - yana sane da matsalolin da suke fuskanta.

Yana daya daga cikin ƴan kasuwar Ghana waɗanda ke da niyyar amfani da wannan dama ta sarrafa koko a cikin ƙasar ta Ghana, kafin fitar da kayayyakin da aka samar.

Amma idan aka zo batun kayan zaki, Nana Aduna "ya yanke shawarar kaucewa cakulan", kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Kayayyakin samar da cakulan suna da tsada, a cewarsa. "kuma ba mu da masana'antar suga da kuma masan'antun cikin gida.

Maimakon haka yana samun kuɗin shiga daga yawon buɗe ido inda baƙi za su iya ganin hanyoyin da ake sarrafa koko har zuwa yadda ake haɗa shayi da giya.

Don yin cakulan, a gefe guda, dole sai Nana Aduna ta shigo da madara da sukari, wanda zai ƙara tsadar aikin.

Ya kuma ce samar da kayan na buƙatar na'urar sanyayawa, amma tsadar kayan aikin don cimma hakan babbar matsala ce ga 'yan kasuwa ba tare da kudade masu yawa ba.

Gahawar da manoma ke samarwa da kuma giya galibi ba a haɗa shi da koko, amma ana ciniki sosai, a cewar Nana Aduna, wanda ya ce zai iya ninka sau 15 zuwa 20 kan waɗannan kayayyakin fiye wake.

Cakulan zai iya samun ƙarin kasuwa sannan kuma ya samar da kyakkyawan sakamako amma a halin yanzu, ya ce hakan ba zai yiwu ba.

Akwai wasu da ke da burin kafa kamfanin sarrafa koko a Ghana amma yanzu suna ɗaukar koko zuwa ƙasashen waje.

Kamfanonin sun haɗa da babban kamfanin Raphael Dapaah ɗan asalin Ghana da Birtaniya, wanda ke Landan.

A 2016, ya yanke shawarar mayar da hankali kan koko inda iyalinsa ke Ghana sama da shekaru 60 da ke tafiyar da kamfaninsa na samar da cakulan.

Yana tace cakulan a masana'antarsa ta Landan wanda ya haɗa abubuwa kamar su garin madarar kwakwa da gishirin teku na tekun Atlantika a Ghana.

Samun kudade babbar matsala ce kuma Nana Aduna ya ce yawan kudin ruwa na banki matsala ce ga ƴan kasuwa masu tasowa kuma a halin yanzu ba zai iya samun rancen kudi ba.

"Ba za ku iya haɓaka kasuwanci ba idan har dole sai ka biya kuɗin tsakanin kashi 18 zuwa 20 ko ma fiye da haka," in ji shi.

Amma gwamnati ta yi alƙawarin magance waɗannan matsalolin.