BBC Hausa of Saturday, 3 April 2021

Source: BBC

Yadda shirin tabbatar da budurci ya fusata gwamnatin Faransa

Ministar 'yan kasan Faransa Marlene Sciappa Ministar 'yan kasan Faransa Marlene Sciappa

Gwamnatin Faransa ta caccaki wani shirin talabijin da ya nuna wani biki da ake yi domin 'yan mata da za su yi aure su tabbatar da budurcinsu ta hanyar amfani da kyalle.

Ministar 'yan kasa Marlene Sciappa ta rubuta wasika ga hukumar kula da kafofin watsa labarai ta kasar tana mai cewa ta fusata a kan yadda shirin ya nuna yadda ake aure a al'ummar Gypsy inda 'yan uwan amarya ke bincikarta kafin a daura mata aure domin tabbatar da budurcinta.

Shirin wanda aka watsa a wata kafar talabijin da ake kira TFX na bibiyar al'adun aure na al'ummar Catalan da ke kudancin garin Perpigan.

Wani bangare na shirin da aka watsa a watan Fabarairu, masu kallo sun ga lokacin da ake shirye-shiryen bikin aure, gadon da za a yi amfani da shi domin tabbatar da budurcin amarya.

Bayanin da aka yi a shirin yace: A kan wannan gadon mace mai horo na musaman ta ke tabbatar ta budurcin amarya. Bikin da aka yi wa lakabi da handkerchief ya samo asali ne daga kakanni da ba za a iya kauce masa ba. Idan Naomi ta yi tarraya da wani, toh za a soke bikin auren.''

Sai dai a wasikar da Madam Schiappa ta rubuta ta ce ta ji haushi a kan yadda aka tsara shirin ba tare da tambayoyi ba.

Ta kuma bukaci majalisar dokokin kasar ta zartar da dokar da ta hana gwajin budurci ga 'yan mata da kuma tabbatar da amincewar wadanda za ayi wa aure.