BBC Hausa of Wednesday, 5 May 2021

Source: BBC

Yadda wata mata ƴar Mali ta haifi jariri tara lokaci guda

Halima Cisse ta haifi jariran - mata biyar da maza huɗu a wani asibiti da ke Morocco Halima Cisse ta haifi jariran - mata biyar da maza huɗu a wani asibiti da ke Morocco

Wata mata ƴar ƙasar Mali ta haifi jarirai tara ta hanyar tiyata a wani lamari da ake iya cewa ba kasafai ake samun irinsa ba.

A ranar Talata ne Halima Cisse - mai shekara 25 a duniya - ta haifi jariran - mata biyar da maza huɗu a wani asibiti da ke Morocco, a cewar ministar lafiya ta Mali Fanta Siby cikin wata sanarwa.

An sa ran Ms Cisse za ta haifi ƴaƴa bakwai bisa hoton cikinta da aka ɗauka a Mali da Morocco wanda bai iya gano cewa akwai karin jarirai biyu ba a cikin matar.

Dr Siby ta ce jariran da mahaifiyarsu na cikin "ƙoshin lafiya". Ana kuma sa ran za su koma gida nan da wasu makwanni.

Ta taya likitocin da suka yi tiyatar a Mali da Morocco waɗanda suka nuna ƙwarewa wajen nasarar aikin.

Juna biyun Ms Cisse ya ja hankalin mutane da shugabannin Mali - inda hukumomi suka fitar da ita zuwa Morocco a lokacin da ta buƙaci kulawar ƙwararru, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar lafiya ta Morocco, Rachid Koudhari ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ba shi da masaniyar irin wannan haihuwar da ta taɓa faruwa a ƙasar.