Hukumar NITDA a Najeriya mai bunƙasa fasahar sadarwa ta shawarci ƴan Najeriya kan yadda ya kamata su yi amfani da dandalin sadarwa na WhatsApp domin su guje wa faɗawa tarkon satar bayanansu
Shawarar ta biyo bayan sabbin dokokin da kamfanin Facebook Incorporated, wanda ya mallaki WhatsApp, ya ƙaddamar a kan dukkan masu amfani da dandalin na ɗibar bayanansu don bai wa sauran kamfanonin da Facebook ya mallaka.
A cikin wata sanarwa, Hukumar NITDA ta yi gargaɗi ga ƴan Najeriya game da rashin karanta ƙa'idojin yarjejeniyar da suke shiga kafin fara amfani da manhajoji da kuma shafukan intanet irinsu WhatsApp.
"Domin fahimtar yadda abin ke aiki, NITDA ta haɗa kai da hukumomin da ke kare bayanan sirri na Afirka don tattaunawa da Facebook, kamfanin da ya mallaki Whatsapp," a cewar hukumar.
NITDA ta shawarci ƴan Najeriya cewa suna da ƴancin daina amfani da WhatsApp ko kuma su daina tura bayanai masu muhimmanci da suka shafi rayuwarsu ta dandalin.
Me sabbin ƙa'idojin suka ƙunsa?
Daga ranar Asabar, 15 ga watan Mayu ne sabon tsarin ƙunshin doka ko kuma Privacy Policy a turance, wanda WhatsApp ya shimfiɗa suka fara aiki a ƙasashe waɗanda da ba sa cikin ƙungiyar Tarayyar Turai ta European Union (EU).
Kamfanin Facebook Incorporated wanda ya mallaki WhatsApp a Fabrairu 2014, zai dinga ɗibar bayanan masu amfani da WhatsApp sannan ya bai wa sauran kamfanonin sada zumunta da Facebook ya mallaka.
Ya zuwa yanzu, Facebook da Instagram haɗi da WhatsApp ne kamfanin ya mallaka.
"A matsayin ɗaya daga cikin kamfanoni mallakar facebook, WhatsApp zai dinga karɓa tare da yaɗa bayanai ga sauran kamfanonin Facebook," in ji facebook.
"Za su iya samun bayanai daga gare mu su ma za su iya ba mu bayanai kuma mu yi amfani da su domin inganta harkokin kasuwanci tsakanin kamfanonin."
Tun asali WhatsApp ya ce hira tsakanin abokai sirri ce babu wanda yake iya gani sai masu ita, amma kuma yanzu ya sauya matsayi game da bayanan da suka shafi mai amfani da dandalin - kamar sunansa da hotonsa - waɗanda yanzu zai iya kwasa ya kai wani wuri.
Bayanan da WhatsApp zai dinga ɗiba daga masu ma'amula da shi
Shawarar yadda za ku kare bayananku
Daga cikin shawarwarin da NITDA ta bayar, ta ce ƴan Najeriya su haƙura da amfani da WhatsApp baki ɗaya don guje wa ɗibar bayanansu.
"Masu amfani da WhatsApp na da zaɓin su yarda a dinga ɗibar bayanansu ko kar su yarda ta hanyar amincewa da waɗannan sabbin ƙa'idoji," a cewar NITDA.
"Na farko, 'yan Najeriya su sani cewa akwai sauran dandali na sada zumunta da ke da dukkan abubuwan da WhatsApp ke da su, waɗanda za su iya komawa.
"Na biyu, ku rage tattauna bayanai da suka shafi rayuwarku ta saƙonnin sirri (inbox) da sauran shafukan sada zumunta, tun da dai yanzu sun sauya alƙawarin da suka yi na sirranta ayyukan mutane saboda neman kuɗi."
NITDA ta ce ta bai wa Facebbok shawara kan hanyoyin da ya kamata ya bi wajen haɓakawa ko kuma inganta amfani da bayanan 'yan Najeriya masu amfani da shafukansa kamar yadda tsarin dokokin kare bayanan ƴan ƙasa wato Nigeria Data Protection Regulation (NDPR) ya tanada.
Shugaban hukumar NITDA, Kashifu Inuwa Abdullahi, ya faɗa wa BBC Hausa cewa: "Mun ƙirƙiri tsarin NDPR ne domin mu tabbatar cewa bayanan ƴan Najeriya masu muhimmanci ba su shiga hannun da bai kamata ba.