Ranar Asabar za a buga wasan karshe a Copa del Rey tsakanin Atheletic Bilbao da Barcelona da za su kara a Estadio La Cartuja da ke Sevilla.
Kungiyoyin biyu sun fafata sau uku a kakar bana:
Spanish La Liga 31 ga watan Janairun 2021
- Barcelona 2 - 1 Atheletic Bilbao
Spanish Super Cup 17 ga watan Janairun 2021
- Barcelona 2 - 3 Atheletic Bilbao
Spanish La Liga 6 ga watan Janairun 2021
- Atheletic Bilbao 2 - 3 Barcelona
Barcelona ce kan gaba a lashe Copa del Rey a Spaniya, mai 30 jumulla, Atheletic Bilbao ce ta biyu mai 23 a tarihi.
Rabon da Barcelona ta dauki kofin tun kakar 2016/17, ita kuwa Bilbao rabon ta da shi tun 1983/1984.
Barcelona tana ta uku a kan teburin La Liga da maki 65, ita kuwa Bilbao tana da maki 37 tana ta 11 a kasan teburin gasar Spaniyar.
Tuni dai kocin Barcelona Ronald Koeman ya gayyaci dukkan 'yan wasan kungiyar zuwa karawar karshen in ban da Philippe Coutinho da ke jinya a Brazil.
Ansu Fati da Neto da ke jinya duk suna daga cikin wadanda Barcelona za ta je da su Sevilla, domin buga wasan na karshe a Copa del Rey ranar Asabar.
'Yan Barcelona da za a je da su gasar Copa del Rey:
Masu tsaron raga: Marc-Andre ter Stegen da Neto (mai yin jinya) da Inaki Pena da kuma Arnau Tenas.
Masu tsaron baya: Sergino Dest da Gerard Pique da Ronald Araujo da Clement Lenglet da Jordi Alba da Sergi Roberto da Samuel Umtiti da Junior Firpo da kuma Oscar Mingueza.
Masu buga tsakiya: Sergio Busquets da Miralem Pjanic da Riqui Puig da Pedri da Matheus Fernandes da Frenkie de Jong da kuma Ilaix Moriba.
Masu cin kwallo: Antoine Griezmann da Martin Braithwaite da Lionel Messi da Ousmane Dembele da Francisco Trincao da Ansu Fati (mai yin jnya).