Real Madrid za ta ziyarci Cadiz ranar Laraba, domin buga wasan mako na 31 a gasar La Liga da za su kece raini a Ramon de Carranza.
A wasan farko da suka fafata a gasar ranar 17 ga watan Oktoban 2020, Cadiz ce ta yi nasara da ci 1-0.
Cadiz din ta zura kwallo a ragar Real Madrid a minti na 16 da fara wasa ta hannun Anthony Lozano.
Real Madrid tana ta biyu a kan teburi da maki 67 da tazarar maki uku tsakaninta da Atletico Madrid mai jan ragama.
Ita kuwa Cadiz mai maki 36 tana ta 13 a kasan teburin gasar ta Spaniya ta bana.
Real Madrid mai rike da kofin La Liga ta kai wasan daf da karshe a Champions League, bayan da ta fitar da Liverpool da kwallo 3-1.
Real din za ta fatra karbar bakuncin Chelsea a gasar ta zakarun Turai a makon karshe na watan Afirilu.
Sannan ta ziyarci Stanford Bridge a makon farko na watan Mayun a karawa ta biyu a Champions League din.
Real Madrid tana cikin kungiyoyi 12 da suke son fara European Super League a Turai, wadda ake ta caccakar wannan sabuwar gasar.
'Yan waasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.
Masu tsaron baya: Carvajal da E. Militao da Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da Chust da kuma Miguel.
Masu buga tsakiya: Casemiro da Isco da Arribas da kuma Blanco.
Masu cin kwallo: Benzema da Asensio da Vini Jr. da Mariano da kuma Rodrygo.
Sauran wasannin mako na 31 da za a buga ranar Laraba:
- Levante da Sevilla
- Osasuna da Valencia
- Real Betis da Athletic Bilbao
- Deportivo Alaves da Villarreal
- Elche da Real Valladolid