BBC Hausa of Friday, 5 March 2021

Source: BBC

'Yan fashi sun kashe mutum 15 a Jihar Sokoto

'Yan bindiga sun kashe mutum 15 a harin da suka kai garin Tara a Jihar Sokoto 'Yan bindiga sun kashe mutum 15 a harin da suka kai garin Tara a Jihar Sokoto

Wasu 'yan bindiga sun kashe mutum 15 a harin da suka kai garin Tara da wasu ƙauyukan da ke kewayensa a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya,

Kazalika ana zargin cewa maharan sun sace wasu dabbobi bayan sun far wa ƙauyukan da tsakar daren Alhamis,

Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun shammaci mutanen ta wata mashiga, inda suka buɗe wuta a kan jama`a tare da kashe mutum 15 sannan mutum bakwai suka jikkata.

Cikin wadanda suka rasu har da wata `yar shekara shida da haihuwa.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, rundunar 'yan sandan Sokoto ba ta amsa kiran wayar da BBC ta yi mata ba, amma mai taimaka wa gwamnan jihar kan kafafen yaɗa labarai, Malam Muhammad Bello, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kazalika, maharan sun yi awon-gaba da shanu masu yawa kuma ba su bar garin ba sai da suka ƙona rumbunan ajiyar abinci.

"Tun ƙarfe 12:00 na dare suka shigo gari suka fara ɓarna har zuwa ƙarfe 2:00," a cewar wani mazaunin yankin da ba amince a bayyana sunansa ba.

Ya ƙara da cewa: "Sun kashe mutum takwas cikin garin Tara, sun kashe huɗu a garin Hillu, sun kashe uku a Nasarawa, sun kashe mutum ɗaya a garin Zago.

"Sanna sun tafi da dukiya kimanin 470 na shanu da dabbobi."

Shi ma wani mazaunin yankin ya ce tuni an yi jana'izar waɗanda suka rasun.

"An yi ta kiran jami'an tsaro a lokacin amma ba su samu zuwa ba kuma ko da suka zo sun riga sun tafi, duka da cewa mutanen gari sun bi su amma ba a iya cim masu ba," in ji shi.

A watan Janairun da ya gabata ma mahara sun far wa yankin, inda suka sace shanu kusan 200.