BBC Hausa of Monday, 10 May 2021

Source: BBC

'Yan sandan Isra'ila sun raunata gomman Falasdinawa

Masu zanga-zangar nuna kin amincewa da shirin gwamnatin Isra'ila na korar Falasdinawa daga gidajensu Masu zanga-zangar nuna kin amincewa da shirin gwamnatin Isra'ila na korar Falasdinawa daga gidajensu

An ci gaba da dauki-ba-dadi a dare na biyu a jere tsakanin Falasdinawa da 'yan sandan Isra'ila a Birnn Kudus, inda aka raunata gomman Falasdinawa.

Masu zanga-zangar nuna kin amincewa da shirin gwamnatin Isra'ila na korar Falasdinawa daga gidajensu don gina wa Yahudawa matsuguni, sun rika jifan 'yan sandan da duwatsu, sannan sun kunna wuta a kofar Damascus Gate da ke Birnin na Kudus.

Rikicin na Asabar da dare a wannan karon ya kara ruruwa ne yayin da dubban Musulmi suka hallara don ibada a Masallacin Birnin Kudus domin daren Laylat al-Qadr, dare mafi girma a wajen Musulmi, a watan Ramadan.

'Yan sandn Isra'ila sun mayar da martini ta hanyar harba gurneti-gurneti da feshi da ruwa ga dimbin masu zanga-zangar da ke jifansu da duwatsu

Kungiyar Agaji ta Red Crescent ta ce an raunata akalla Falasdinawa 80, daga ciki an nufi asibiti da 14, yayin da 'yan sandan Isra'ila suka ce suma an raunata musu jami'i daya.

Kamar yadda tarzomar ta samo asali, ta ci gaba ne kan shirin gwamnatin Israila na korar Falasdinawa daga muhallinsu domin gina wa Yahudawa 'yan kama wuri zauna gidaje.

A ranar Juma'a a rikici mafi muni cikin shekaru, an raunata sama da Falasdinawa 200 da 'yan sandan Isra'ila akalla 17 kamar yadda ma'aikatan lafiya da 'yan sandan Isra'ila suka bayyana,

a rikicin a kusa da Masallacin Birnin Kudus, wanda wuri ne mai tsarki ga Musulmi da kuma Yahudawa, da ake yawan samun rikici tsakanin bangarorin biyu,

Tun da farko a ranar Asabar din 'yan sandan Isra'ila sun hana gomman motocin safa-safa da ke dauke da Musulmi da ke zuwa Masallacin na kudus domin ibada, daman kuma sun kama Falasdinawa da yawa bayan rikicin na Juma'a.

Yayin da Musulmin ke kokawa da cewa 'yan sandan sun hana su shiga Masallacin ne domin hana su ibada, Firaministan Isra'ilar Benjamin Netanyahu ya ce kasar na yin abin da ya dace ne ta tabbatar da bin doka da oda, tare da mutunta 'yancin yin addini.

Shi kuwa jagoran Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi Allah-wadarai da abin da ya kira hare-haren laifi na Isra'ila.

Tun a yakin Gabas ta Tsakiya na shekarar 1967 ne Isra'ila ta mamaye yankin Gabashin Kudus, kuma tun daga sannan take daukar birnin gaba daya a matsayin babban birnin kasarta, duk da cewa yawancin kasashe da hukumomin duniya bas u amince da hakan ba.

Falasdinawa na daukar yankin na Gabashin Birnin Kudus a matsayin inda zai kasance babban birnin kasarsu mai 'yanci da suke fata za su samu a nan gaba.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Isra'ila da ta dakatar da duk wani shiri nata na korar Falasdinawa daga yankin, ta kuma daina amfani da karfin tsiya a kan masu zanga-zanga.

A ranar Litinin Kotun Kolin Isra'ila za ta saurari kara a kan dambarwar da aka dade ana yi kan wannan yanki.

Kungiyar Kasashen Larabawa ta League of Arab States ta yi kira ga kasashe da hukumomin duniya da su shiga lamarin su hana Isra'ila tashin Falasdinawan daga gundumar da ake kira Shaikh Jarrah a yankin gabashin birnin Kudus din.

A ranar Litinin ne ake sa ran Kotun Kolin Isra'ila za ta saurari kara a kan shari'ar da aka dade ana yi kan batun.