BBC Hausa of Sunday, 21 March 2021

Source: BBC

'Yan sandan Najeriya sun fara binciken yunƙurin halaka gwamnan Benue Samuel Ortom

Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu

Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu ya bayar da umarnin tsaurara tsaro ga Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue bayan da wasu 'yan bindiga suka yi yunƙurin kashe shi.

Mai magana da yawun rundunar ya ce Mohammed Adamu ya umarci a ƙaddamar da cikakken bincike game da harin.

Da tsakar ranar Asabar ce wasu 'yan bindiga suka kai wa tawagar Gwamna Samuel Ortom hari a gidan gonarsa da ke kan hanyar Makurdi zuwa Gboko, kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

"Sufeto janar ya umarci kwamishinan 'yan sandan Benue ya gudanar da cikakken bincike don hukunta mutanen da binciken ya gano," in ji kakakin 'yan sandan Frank Mba.

Ya ƙara da cewa babban sufeton ya tura tawagar bincike ta musamman daga sashen binciken laifuka na Abuja wato FCID domin gaggauta gudanar da binciken.

Rahotanni sun ce jami'an tsaron gwamnan sun yi musayar wuta mai zafi da maharan yayin da tawagarsa ke kan hanya5r komawa gida daga Gboko.

Benue na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren 'yan bindhiga masu garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.

Harin na matsorata ne kuma na ƙeta - Gwamnonin Najeriya

Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana harin a matsayin "abin kiɗimarwa wanda matsorata suka kai".

Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ya fitar a yau Lahadi, NGF ta taya Ortom alhini game da harin da ta ce "na tsoro ne kum na ƙeta".

"NGF na faɗa da babbar murya cewa yunƙurin da ake yi na ɗaiɗaita Jihar Benue ba zai yi nasara ba," a cewar sanarwar.

"A kwanan nan aka kashe ɗaya daga cikin 'yan uwan wani tsohon gwamnan jihar. Wajibi ne a kawo ƙarshen iirin wannan aikin na tashin hankali bisa kowane irin dalili domin kashe mazauna Benue."

Shugabannin da suka tsallake rijiya da baya

A baya-bayan nan, an kai wa wasu shugabanni da suka haɗa da gwamnoni da sarakunan gargajiya hari, inda suka sha da kyar.

A watan Satumban 2020, masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiyar IS sun kashe jami'an tsaro 15 a wani kwanton-ɓauna da suka yi wa tawagar Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum.

Daga cikin waɗanda suka rasa ransu a harin akwai 'yan sanda takwas da sojoji uku da kuma 'yan kungiyar 'yan sintiri da ke tallafa wa dakarun gwamnati wato Civilian JTF guda huɗu.

Zulum da tawagarsa na kan hanyarsu ne ta zuwa garin Baga a lokacin da aka kai musu harin.

Sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II ya fuskanci harin 'yan bindigar ranar Litinin, 15 ga Maris lokacin da suka buɗe wa motarsa wuta.

Sai dai basaraken ba ya cikin motar lokacin da lamarin ya faru.

A hirarsa da BBC, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II ya ce shi aka nufa da harin amma aka kuskure.