Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a karawar mako na 30 a gasar La Liga da za su fafata ranar Asabar a Alfredo Di Stefano.
A wasan farko na hamayya da ake kira El Clasico da suka yi ranar 24 ga watan Oktoba, Real ce ta yi nasara da ci 3-1 a Camp Nou.
Barcelona ce ta biyu a kan teburin La Liga da tazarar maki daya tsakaninta da Atletico ta biyu, Real tana ta uku da tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona.
Rabon da Barcelona ta yi rashin nasara a gasar La Liga tun wanda Cadiz ta doke ta 2-1 ranar 5 ga watan Disamba.
Sai dai Tuni Paris St Germain ta yi waje da Barcelona a Champions League karawar kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.
Real Madrid kuwa ta doke Liverpool 3-1 ranar Talata a wasan farko zagayen quarter finals da suka yi gumurzu a Alfredo Di Stefano.
Tuni kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 19 da za su fuskanci Barcelona.
'Yan kwallon Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.
Masu tsaron baya: E. Militao da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da kuma Isco.
Masu cin kwallo: Benzema da Asensio da Lucas V. da Vini Jr. da Mariano da kuma Rodrygo.
Shima mai horar da Barcelona, Ronald Koeman ya fayyace 'yan wasa 23 da za su kara da Real ranar Asabar.
'Yan wasan Barcelona:
Ter Stegen da Dest da Pique da R. Araujo da Sergio da Griezmann da Pjanic da Braithwaite da Messi da O. Dembele da Riqui Puig da Lenglet da kuma Pedri.
Sauran sun hada da Trincao da Jordi Alba da S. Roberto da F. De Jong da Umtiti da Junior da Inaki Pena da Ilaix Moriba da O. Mingueza da kuma Arnau Tenas.