BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

Yau ne Mahamane Ousmane zai kalubalancin sakamakon zabe a Nijar

Mahamane Ousmane (dama) zai kalubalance nasarar Mohamed Bazoum Mahamane Ousmane (dama) zai kalubalance nasarar Mohamed Bazoum

Ranar Litinin ɗin nan ake sa ran ɗan takarar jam'iyyar adawa ta RDR-Tchanji a Jamhuriyyar Nijar Mahamane Ousmane zai shigar da ƙara gaban Kotun tsarin mulki ta kasar don ƙalubalantar sakamankon zaɓen watan Fabrairu, wato zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da ya gabata.

Tun a farko Hukumar zaɓen ƙasar wato CENI ta ayyana abokin fafatawar Mahamane na jam'iyyar PNDS mai mulki, Bazoum Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban kasa zagaye na biyu da ƙuri'u sama da miliyan biyu da rabi.

To sai dai, take yanke Mahamane Ousmane ya yi watsi da sakamakon zaben, abun da ya janyo barkewar wata babbar tarzoma da zanga-zanga a birnin Yamai da kewaye.

Magatakardar jam'iyyar ta RDR-Tchanji Doktor Abdu Sani, ya ce suna zargin cewa an tabbka magudi, tare da bayar da musalin cewa jam'iya mai mulki ta PNDS-Tarraya ta yi aringizon kuri'u sama da 900,000. a wasu garuruwa da suka hadar da jihar Tahoua da Agadez da kuma yankunan arewacin jihar Maradi da ta Damagaram.

Ita dai hukumar zaɓe ta CENI ta yi nata aikin, kuma ta bayyana Bazoum a matsayin wanda ya samu nasara, abin jira a gani shine ko kotun tsarin mulki da ke da alhakin tabbatar da wanda aka zaba za ta yi hakan ko kuwa za ta yi watsi da nasararsa.

Tun kafin zuwan lokacin zaɓen yan adawa a Nijar sun bayyana rashin gamsuwa da hukumar zaɓrn ƙasar, saboda zargin da suke yi na cewa galibin manyanta yan jam'iya mai mulki ne.

To amma a nasu bangaren masu mulki na ganin cewa bai kamata yan adawa su cika gari da surutu ba, zai fi kyautuwa su gabatarwa kotu gamsassun hujjojin da za su tabatar da cewa an yi magudi a zaben, kamar yadda suke zargi.

Rikicin bayan zaɓe

An samu gagarumin tashin hankali bayan sanar da sakamakon karshe na zaben shugaban ƙsar, har ta kai ga matasa suk yi kone-kone da fashe-fashen motoci da wawasar dukiyar jama'a.

Wannan al'amari ya sa hukumomin kasar ta jamhuriyar Nijar daukar wasu matakai masu tsauri, saboda fargaba da tsaron abin da kaje ya zo.

Daga cikin matakan da gwamnati ta dauka sun hada da kama madugun 'yan adawa Hama Amadou da wasu 'yan bangaren adawar kamar tsohon hafsan-hafsoshin kasar Janar Moumouni Boureima da ake kira da suna Tchanga da Kanal Habou Oumarou da Maman Ousseini da dai sauren wasu jiga-jigan bangaren jam'iyun adawar kasar.

Aƙalla an kama mutane sama da 400 wadanda gwamnati ke zargin suna da hannu a rikicin da aka samu.

Haka nan gwamnatin Nijar ta dauki matakin datse hanyoyin sadarwa na intanet a fadin kasar baki daya, wanda daga bisani ta maido bayan an shafe kwanaki sama da 10