Hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA za ta binciki Zlatan Ibrahimovic kan zargin hada hannun mallakar wani kamfanin caca.
Wasu rahotanni daga Sweden na cewar dan kwallon AC Milan, mai shekara 30 ya karya ka'idar hukumar, bayan da ya yi hadakar mallakar kamfanin caca.
Dokar hukumar kwallon kafar Turai ta fayyace cewar kada dan wasa ya saka jari ko hannu a kamfanin caca.
A makon jiya ne Ibrahimovic ya tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a AC Milan, bayan da ya cika shekara 40 da haihuwa.
Tsohon dan wasan Manchester United ya ci kwallo 17 a wasa 25 a dukkan fafatawar da ya yi a kakar bana.
Ibrahimovic ya koma buga wa tawagar kwallon kafa ta Sweden tamaula, bayan shekara biyar da yin ritaya.