BBC Hausa of Monday, 22 March 2021

Source: BBC

Zaben Nijar: Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar Bazoum Mohamed

Mohamed Bazoum zai gaji shugaba Mahamadou Issoufou Mohamed Bazoum zai gaji shugaba Mahamadou Issoufou

Kotun ƙolin Jamhuriyyar Nijar ta tabbatar da Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar Nijar da aka yi zagaye na biyu.

Bazoum Mohamed na jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya, da ya ci zaben da kashi 55.66 cikin 100 na kuri'un da aka jefa zai gaji shugaba Mahamadou Issoufou da ya rike ragamar mulkin kasar na tsawon shekara 10.

Kotun tsarin mulkin dai ta bawa Bazoum, tsohon ministan cikin gida 55.6 na kuri'un da aka kada, abin da ke nufin ya zarce tsohon shugaban kasar Mahamane Ousmane, wanda ya samu kashi 44.34.

Ranar da za a rantsar da shi wato 2 ga watan Afrilu, za ta kasance rana mai cike tarihi, inda wani shugaba da aka zaɓa ta hanyar dimukradiyya zai mika mulki ga wani, da shima aka zabe shi ta wannan hanya.

Cikin wata sanarwar kotun, ta ce ta soke sakamakon zaben daga rumfunan zabe 73, ba tare da ta fadi dalilin yin hakan ba, abin da ya janyo rage tasirin nasarar Bazoum Muhammad.

Sanarwar ba ta ba da amsa kai tsaye kan zargin Ousmane na cewa an yi magudi a zaben ba, zargin da ya haifar da mummunar zanga-zanga a Yamai babban birnin kasar a watan jiya.

Aƙalla mutane biyu sun mutu kuma an kama daruruwa bayan barkewar zanga zangar da ta biyo bayan sanar da sakamakon zaben shugaban ƙasa da mahukunta suka yi.