BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021
Source: BBC
Wani babban jami'in Senegal wanda aikinsa shi ne sasanta rikici ya ce ƙasar tana kan mummunar turba bayan shafe kwana hudu ana zanga-zangar da ta yi sanaidn mutuwar mutum biyar.
Alioune Badara Cissé, wanda aka fi sani da mai sasantawa, ya nemi hukumomi da su daina yi wa masu zanga-zanga barazana da tsoratar da su.
Ya kuma yi kira ga masu boren a kan tituna da su yi komai cikin lumana ba tare da sace-sace ba.
Rikicin ya samo asali ne bayan kama wani jagoran adawa Ousmane Sonko.
Mr Sonko ya bayyana a gaban kotu a ranar Juma'a, inda ake tuhumarsa da jawo rikici a tsakanin al'umma. Ana kuma tuhumarsa da fyaɗe.
Ya yi watsi da dukkan tuhumar sannan magoya bayansa sun ce zarge-zargen bi-ta-da-ƙullin siyasa ne.
Rashin daidato a bangaren tattalin arziki da yanayin rayuwa ya sake tunuzra matasan da ke zanga-zangar.
A wani taron manema labarai a ranar Lahadi, Mr Cissé ya ce hukumomi "na buƙatar dan dakatawa su yi magana da matasa" ya kuma yi gargaɗi cewa "muna daf da faɗa wa cikin wata masifa ta rugujewa".
Maganar tasa na zuwa ne kwana daya bayan da wani matashi a birnin Diaobe da ke kudancin kasar ya zamo mutum na biyar da ya mutu a rikicin da aka yi tsakaninsu da dakarun tsaro a sassan ƙasar da dama.
Amma mai sasancin ya yi gargadin cewa ƙasar na fuskantar rikici idan har gwamnati ba ta yi wani abu da gaggawa don magance tsananin talaucin da ake ciki da kuma rashin aikin yi ga matasa ba, a cewar editan Afirka na BBC Will Ross.
Bayan artabun da aka yi a ranar Juma'a a Dakar babban birnin ƙasar, Ministan Harkokin Cikin Gida Antoine Felix Abdoulaye Diome, ya sha alwashin amfani da "duk hanyar da ta dace don dawo da doka da oda."
Da yake magana a tashar talbijin, ta ƙasar Mr Diome ya zargi Mr Sonko da "yin kiraye-kirayen ta da rikici".
Gamayyar ƴan hamayyar mai suna Movement to Defend Democracy (M2D), wacce ta assasa zanga-zangar, ta sanar da cewa za a ci gaba da yin zanga-zangar ta tsawon kwana uku daga ranar Litinin.
Ƙungiyar hadin kan ƙasashen Afirka Ta Yamma Ecowas ta yi Allah-wadai da rikicin tare da kira ga dukkan ɓangarorin da su yi haƙuri su janye" - inda ya ƙara da cewa ya kamata hukumomi su "ɗauki dukkan matakan da suka dace don kawo zaman lafiya da tabbatar da ƴancin yin zanga-zanga cikin lumana".
An zargi Sonko mai shekara 46 da aikata fyaɗe a watan Fabrairu.
An kama shi a ranar Laraba sakamakon binciken da aka yi, sannan aka kai shi kotu tare da wasu magoya bayan ƙungiyar tasa.
Ƴan sanda sun ce sai suka kama shi saboda jawo rikici bayan da ya ƙi sauya hanyarsa ta zuwa kotun.
Mr Sonko ya ce zarge-zargen fyaɗen ƙarya ne. Ya zargi Shugaba Macky Sall da ƙoƙarin kawar da ƴan adawa gabanin zaɓen shekarar 2024.
An cire sunan ƴan adawar biyu daga jerin masu takara a zaben 2019 bayan da aka tuhume su, abin da suka kira bi-ta da ƙullin siyasa.
Akwai rahotannin da ke cewa Mista Salla na iya sauya kundin tsarin mulki don ba shi damar sake tsaywa takara a karo na uku.
Mr Sonko - wanda ya yi tashe sosai a tsakanin matasan Senegal - shi ne kaɗai dan adawa mai karfi da ya zama kalubale ga shugaban kasar, kamar yadda Ndèye Khady Lo ta Sashen BBC Afrique da ke Dakar ta bayyana.
A shekarar 2014 ya samar da jam'iyyar siyasarsa, Pastef-Les Patriotes, ya kuma zo na uku a zaben shekarar 2019 da kashi 15 cikin 100 na ƙuri'un.