Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya musanta rahotannin da ke cewar zai bar kungiyar a karshen kakar bana.
Kocin ya fadi haka ne, bayan kammala wasan da Real Madrid ta je ta doke Athletic Bilbao da ci 1-0 a wasan mako na 37 a gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadi.
Real Madrid wadda ke takarar kare kofin La Liga, tana mataki na biyu da maki 81 da tazarar maki biyu tsakaninta da Atletico mai jan ragama.
Sai a ranar Lahadi 23 ga watanm Mayu za a karkare wasannin mako na 38 kuma na karshe a gasar La Liga ta bana, shi ne za a tantance wadda za ta lashe kofin kakar 2020/21.
Zidane ya ce ya mayar da hankalinsa kan wasan da Real za ta karbi bakuncin Villareal ranar Lahadi a gasar ta La Liga.
Tun farko wasu jaridu ne a Spaniya suka wallafa cewar kocin ya shaida wa 'yan wasa cewar a kakar bana zai bar kungiyar - batun da ya ce ba gaskiya ba ne.
Zidane ya ja ragamar Real karo na biyu kenan, bayan da ya lashe Champions League uku a jere daga lokacin da ya fara aiki tsakanin 2016 zuwa 2018.
Ya koma horar da Madrid karo na biyu, bayan da kungiyar ta sallami Julen Lopetegui da kuma Santiago Solari, daga nan ya lashe La Liga a bara kakar 2019/20.
Sai dai kuma wasu na hasashen cewar watakila idan bai dauki kofi ba a kakar nan zai fuskanci kalubale daga wajen mahukuntan kungiyar.
Real ta rasa Copa del Rey da Spanish Super Cup da kuma Champions League wanda Chelsea ta fitar da ita a kakar nan.