BBC Hausa of Tuesday, 16 March 2021

Source: BBC

Zidane ya gaji da yawan raunin da Eden Hazard ke yi

Dan kwallo Eden Hazard Dan kwallo Eden Hazard

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya ce ba zai iya cewa komai ba, kan yawan raunin da Eden Hazard ke yi a koda yaushe.

Hazard mai shekara 30, ya shiga wasan da Real ta yi nasara a kan Elche da ci 2-1 ranar Asabar a gasar La Liga, saura minti 15 a tashi daga karawar.

Sai dai dan kwallon tawagar Belgium ya kara yin rauni, kuma ba zai buga wa Real Champions League wasa na biyu da Atlanta ranar Talata ba.

Hazard ya buga wasan La Liga 25 tun lokacin da ya koma taka leda a Real Madrid daga Chelsea a 2019, yayin da yake ta fama da yin jinya.

Zidane na fatan dan kwallon zai murmure cikin sauri domin ya ci gaba da buga wa kungiyar wasanni, amma kocin na mamakin yawan raunin da dan kwallon ke yi.

Shima Casemiro ba zai yi wa Real karawar Champions League da Atalanta ba, bayan da dan kwallon Brazil din ya karbi katin gargadi a fafatawar farko a Italiya.

Sai dai kuma kyaftin din kungiyar, Sergio Ramos wanda ya buga wa Real wasan La Liga da Elche ranar Asabar, zai kuma fuskanci Atalanta ranar Talata.

Real za ta karbi bakuncin Atalanta a karawa ta biyu a Champions League, bayan da ta ci 1-0 a Italiya, kuma Ferland Mendy ne ya ci kwallon.