BBC Hausa of Tuesday, 1 June 2021

Source: BBC

Zinedine Zidane ya fadi dalilin da ya bar Real Madrid

Zinedine Zidane ya ajiye aikinsa a masayin kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ajiye aikinsa a masayin kocin Real Madrid

Zinedine Zidane ya ce ya bar aikin horar da Real Madrid, saboda yana jin cewar kungiyar ''ta yanke ƙauna'' a kansa.

Dan kasar Faransar ya bar aikin jan ragamar Real a karo na biyu ranar 27 ga watan Mayu, bayan da ya kasa lashe kofi a kakar 2020/21.

A baya dai Zidane ya fara kocin Madrid a 2016 zuwa 2018, sannan ya koma kan aikin a karo na biyu a Maris din 2019.

"Na bar kungiyar, ba wai na gaji da aikin horar da tamaula ba'' in ji Zidane mai shekara 48.

A wata budaddiyar wasika zuwa ga magoya baya da jaridar Sifaniya, AS ta wallafa ya kara da cewar ''Na bar Real saboda kungiyar ta yanke ƙauna kan aikina, ko kasa taɓukawa kan gina wani abu matsakaici ko mai dogon zango don samun ci gaba.

''Na kwan da sanin ƙwallon ƙafa na kuma san bukatun babbar kungiyar kamar Real Madrid. Na san cewar idan ba ka lashe kofi to ya kamata ka hakura.

''An haife ni da yin nasara, kuma ina kungiyar ne domin na lashe kofuna, amma wani mahimmin batu shi ne magoya bayan da muradunsu, kuma ina da tabbacin cewar ba a daukar wannan kudurin.

''Ana cin karo da koma baya idan aka kasa fahimtar wadannan abubuwa na kara karfin kungiyar.''

Tsohon dan kwallon tawagar Faransa wanda ya yi wa Real wasa tsakanin 2001 zuwa 2006, ya lashe Lashe Champions League uku a jere da La Liga a farkon karbar aikin horar da kungiyar.

Ya kuma lashe La Liga a lokacin da ya karbi aikin jan ragamar kungiyar karo na biyu a kakar 2019/20, kuma saura kwantiragin shekara daya ya rage masa a Real Madrid.

Zidane ya fara cewar shekara 20 da ya yi a Bernabeu ''shi ne abu mafi kayatarwa da ya faru'' a rayuwarsa, kuma a ''ko da yaushe'' zai ci gaba da godewa shugaban Real Florentino Perez.

''Ina kaunar a ci gaba da martabar nasarorin da muka samu tare a kungiyar. Zan so alakata da kungiyar da kuma shugaban nan da watanni ta sauya ta kuma zama ta banbanta da sauran masu horar da tamaula,'' in ji Zidane.

''Ba a tambaya ta alfarma, ko kadan. A wannan lokacin da muke ciki rayuwar koci ba ta wuce kaka biyu a kungiya kar ka dada kar ka rage.

''Idan har kana son alaka ta dade da akwai batutuwa manya da suka fi kudi mahimmaci ko neman suna. Saboda haka dole ne a kula da su.''