Fafaroma Francis ya isa ƙasar Iraƙi a matsayin mai riƙe da muƙamin na farko da ya taɓa zuwa ƙasar a balaguronsa na farko bayan ɓarkewar annobar cutar korona.
Cutar ta korona da kuma matsalolilin tsaro sun sa wannan ziyara tasa ta zama mafi haɗari, sai dai dattijon mai shekara 84 ya haƙiƙance cewa "aikinsa ya je yi".
Zai yi ƙoƙari wurin ƙarfafa wa Kiristocin ƙasar gwiwa, waɗnda ba su da yawa, sannan ya haɗa tattaunawa tsakanin shugabannin addinai ta hanyar yin wata ganawa da babban malamin 'yan Shi'a.
An girke jami'an tsaro kusan 10,000 domin bai wa Fafaroman tsaro, yayin da ake tsaka da dokar hana fita ta awa 24 domin yaƙi da yaɗuwar cutar korona.
Da yake kan hanyarsa ta zuwa Iraƙi, Fafaroma Francis ya ce yana farin cikin sake yin balaguro. "Wannan balaguro ne na musamman zuwa ƙasar da mutane da yawa suka yi shahada a tsawon shekaru," a cewarsa.
Tun farko ya ce bai kamata a sake yin "watsi da Kiristocin Iraƙi ba a karo na biyu", bayanj Fafaroma John Paul ya soke ziyarar da ya shirya kaiwa a 1999 bayan tattaunawa da Shugaan Iraƙi na lokacin Saddam Hussein ya ɓalɓalce.
A cikin shekara 20, yawan ɗaya daga cikin al'ummar Kiristoci mafiya daɗewa a duniya ya ragu daga miliyan ɗaya da 400,000 zuwa kusan 250,000 - ƙasa da kashi ɗaya kenan cikin 100 na al'ummar baki ɗayanta.
Da yawa daga cikinsu sun gudu ƙasashen waje domin tsere wa tashin hankalin da ya turnuƙe ƙasar tun bayan yaƙin da Amurka ta ƙaddamar a 2003, wanda ya yi sanadiyyar tumɓuke Saddam daga mulki.
Kazalika, dubbai ne suka tsere bayan ƙungiyar IS ta fatattaki garuruwa a 2014, inda ta lalata coci-coci masu ɗumbin tarihi tare da ƙwace gidajensu kuma ta sanya musu haraji da kashe waɗanda suka ƙi shiga Musulunci kuma suka zauna a garin.
Me Fafaroman ke son cimmawa?
Shugaban ɗariƙr Katolikan na da burin ƙarfafa wa Kiristocin da aka ci zarafi gwiwa sannan ya yi kiran da a zauna lafiya a ganawar da zai yi da 'yan siyasa da shugabannin addinai, a cewar wakilin BBC Mark Lowen wanda ke cikin tawagar Fafaroman.
Da yake yi wa mutanen Iraƙi jawabi a jajiberin tafiyar tsa, Fafaroma ya ce zai je ne "a matsayin mai aikin ibada, wanda zai nemi afuwar Ubangiji da sasantawa bayan shekarun da aka shafe ana yaƙi da kuma ta'addanci".
Kiristoicin da gwamnatin Saddam ta bai wa tsaro sun fuskanci hare-hare a daga dakarun 'yan bindiga.
Wani hari da aka kai kan Cocin Syriac Catholic a Bagadaza a 2010 ya yi sanadiyyar mutuwar Kiristoici 52. Fafaroma zai kai ziyara cocin ranar Juma'a.
Sai dai shekarun da suka biyo bayan saukar Saddam daga mulkin na cike da tashin hankalin da ya shafi dukkan addinai a faɗin ƙasar akasari tsakanin 'yan Shi'a masu rinjaye da kuma 'yan Sunni marasa rinjaye.
Su wane ne Kiristocin Iraƙi?
Mutanen da ke zaune a ƙasar da ake kira Iraƙi sun shiga Kiristanci tun a ƙarnin farko bayan haihuwar Annabi Isa
A cewar gwamnatin Amurka, Kiristocin da suka rage a Iraƙi ba su fi 250,000, inda al'umma mafi girma ta kusan mutum 200,000 ke zaune a yankin Nineveh Plain da Kurdistan a arewacin ƙasar
Kusan kashi 67 cikin 100 na mutanen Chaldean Catholic ne, wadda ke da nata mabiyan amma take yi wa Fafaroma biyayya. Wasu kashi 20 na mutanen mambobin Cocin Assyrian ne a gabashin ƙasar, waɗanda aka yi imanin sun fi kowa daɗewa a Iraƙi
Sauran su ne Syriac Orthodox, Syriac Catholic, Armenian Catholic, Armenian Apostolic, Anglican, Evangelical da kuma Protestants
Me Fafaroma zai gabatar?
Saboda annobar korona da kuma matsalar tsaro, Fafaroma ba zai haɗu da mutane sosai, a cewar wakilin BBC.
Shi kansa Fafaroman za a yi masa allurar rigakafi ta BioNTech/Pfizer kuma su ma tawagarsa za a yi musu. Sai dai ana ganin balaguron nasa zai jawo yaɗuwar cutar saboda irin cincirundon da za a yi.
A ranar Asabar, Fafaroma zai je garin Najaf wurin 'yan Shi'a, inda zai ziyarci Ayatollah Ali al-Sistani. Jagoran mai shekara 90 wani abin dogaro ne ga miliyoyin 'yan Shia a Iraƙi da sauran wurare.
Fafaroma Francis zai halarci taron mabiya addinai daban-daban a Ur, wani wurin mai ɗumbin tarihi da aka yi imanin cewa nan ne wurin da aka haifi Annabi Ibrahim.
Ranara Lahadi kuma zai je garin Mosul. Zai yi wa waɗanda yaƙin IS ya shafa a Cocin Square, wanda ya jawo kisan dubban fararen hula.
Haka nan, zai gudanar da taron addu'a wato Mass a filin wasa na Irbil, inda ake sa ran dubban mutane za su halarta.