BBC Hausa of Thursday, 15 April 2021

Source: BBC

Ƴan Birtaniyan da ba sa goyon bayan tsarin masarauta

Yarima Philip tare da Sarauniyar Ingila Yarima Philip tare da Sarauniyar Ingila

Bayan rasuwar Yarima Philip, an yi jimamin mutuwarsa a faɗin duniya, tare da nuna goyon baya ga Gidan Sarautar Birtaniya.

Amma yayin da wasu da dama ke taya gidan sarautar Birtaniya jimami da nuna tausayi, ba kowa ba ne a cikin Birtaniya ke goyon bayan masarautar ƙasar.

Lokacin da aka tambaye su, yawancin mutane sun ce suna daraja al'ada da martabar gidan sarautar kuma za su yi baƙin ciki idan ta shafe, amma kuma akwai ƴan Birtaniya da dama da suke son sake fasalta tsarin mulki da zai bayar da damar zaɓen shugaban ƙasa.

Sakamakon ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da YouGov ya gudanar a watan da ya gabata, kashi 63 sun amince a ci gaba da tafiya da tsarin masarauta a Birtaniya.

Yayin da kuma ɗaya daga cikin huɗu suka ce sun fi son a ce akwai zaɓaɓɓen shugaban ƙasa amma akwai ɗaya cikin 10 da ba su da zaɓi.

Birtaniya da Sarauniya Elizabeth ta II mai shekara 94 ke jagoranta, masarautar ta yi mulki kusan shekara 1,000 - baya ga wani gajeren shugabanci na shekara biyar a ƙarni na 16 bayan yaƙin Basasa na Ingila.

Kundin tsarin mulki ya ba Sarauniya ƙarfi da yawa da suka da haɗa da sanya hannu kan doka da naɗa Firaminista da soma zama a majalisa, amma yawancin ikon ana bayar da wakilci a lokaci-lokaci.

Sarauniya Elizabeth kuma ta kasance shugabar ƙasashe 54 na renon Ingila (Commonwealth) waɗanda Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka.

"Ni a ra'ayina ina ganin ba ma bukatar tsarin masarauta. Ban san manufarsu ba kuma hakan wani reshe ne na mulkin mallaka a wani lokaci na daban," in ji Kirsten Johnson ta jami'ar Derby.

"Idan ka tuna lokacin da Sarauniya Elizabeth ta zama sarauniya, ba a daɗe da kammala yaƙin duniya ba kuma a lokacin Commonwealth na cikin wani yanayi na daban.

"Muna da jami'ai da muka zaɓa, don haka ban ga dalilin da ya sa muke buƙatar tsarin masarauta ba," a cewarta.

"Bisa ƙa'ida dole ne Sarauniya ta sanya hannu kan komi, amma a zahiri shugaba ce kawai, kuma mai matuƙar tsada."

A 2020, kuɗin da ake kashe wa masarautar Birtaniya daga kuɗaɗen da mutane ke biyan haraji ya kai fam miliyan 69.4, kamar yadda alƙaluman da hukumar da ke kula da harakokin masarautar ta fitar - alƙaluma mafi girma a tarihi.

Ana kiran kuɗaɗen kyautar Sarauniya da ake amfani da su wajen ɗaukar nauyn ayyukan Sarauniya hidimomin iyalinta da tafiye-tafiye na masarautar da kula da gidajen sarautar, da suka ƙunshi har da akin gyaran fadar Buckingham da aka yi a kwanan nan da kuma gyaran gidan da Yarima Harry da matarsa Meghan suka zauna.

"Kuɗaɗen masu biyan haraji suna zuwa ne matsayin tallafi ga masu sarauta, waɗanda saboda sarautarsu suke amun aiki, da kuɗaɗe na kariya da sauransu, amma me suke yi wa ƙasa?

Ba wai ina cewa ba su yin komi ba ne, amma wane aiki suke da har yake da muhimmanci da kuma alaƙa da masarauta da wani daga waje ba zai iya yi ba," in ji Kirsten.

"Sarauniya Elizabeth ta yi dogon zamani kuma ta yi hakan cike da alhairi.

Ta nuna mace ce mai mutunci, amma ban ga buƙatar sarauniya ba a yanzu ban da yawon buɗe ido, kuma mutanen da ke son zuwa domin ganin Fadar Buckingham na iya ci gaba da zuwa ko da kuwa babu Sarki."

Sarauniya da yawancin iyalinta an ɗauke su a matsayin 'ma'aikatan masarauta' kuma suna aiwatar da ayyukan masarautar sama da 2,000 a kowace shekara a cikin Birtaniya da ƙasashen waje.

Matsayinsu yana nufin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kwanciyar hankali ta hanyar jama'a da ayyukan jin-ƙai.

"Ina kallon gidan masarautar a matsayin waɗanda suka samu dama waɗanda aka haifa a cikin ayyukansu kuma ba za ka iya sauya su ba," in ji Sammy Knight.

Wadda aka haifa ta girma a Canada, kuma ƴar ƙasar Birtaniya, Sammy ta yi imanin cewa tsarin sarauta nan gaba ba zai dace da makomar Birtaniya ba da Commonwealth.

"Ra'ayina shi ne sarauta a matsayin tafarkin shugabanci zai tabbata ne ga Sarauniya," a cewarta.

"Ban damu da sarautar ba, amma ina ganin ita mace ce mai burgewa. Ban ji daɗin ganin yadda Yarima Phillip ya tafi ba saboda ita.

"Ina jin daɗin ayyukan Sarauniya da Duke na Edinburgh - sun yi rayuwa mai ban mamaki kuma ina ganin sun yi sadaukarwa ga hidimar jama'a duk da shekarunsu.

"Ba na son masu tasowa a masarautar kuma ina ganin yanzu lokaci ne da ya kamata a Birtaniya a samu zaɓaɓɓen shugaba."

Lokacin da aka samu saɓani a kuri'un jama'a akwai babban bambanci tsakani yanzu da shekarun baya.

Waɗanda ke tsakanin shekara 18 zuwa 24 su ne mafi ƙarancin tunani kan tsarin masarauta a Birtaniya, yayin da waɗanda suka haura shekara 65 ke goyon bayan riƙe tsarin.

Haka kuma akwai rashin daidaituwa a sakamakon ƙuri'ar idan aka duba yankuna daban-daban na Biritaniya. Kusan rabin mutanen Scotland sun nuna kyakkyawan ra'ayi game da makomar masarautar.

"A matsayina na mutumin Scotland masarautar ba ta kasance baƙuwa gare ni ba," in ji Mathew Burton-Webster, ma'aikacin wata cibiyar kula da ƙananan yara ta Kirkaldy a gabashin gaɓar ruwan Scotland. Abin da kawai muke tunawa a nan shi ne kan kuɗinmu ko kuma idan ɗayansu ya mutu."

"Sun ba kansu sarauta wurare da dama a Scotland da kuma yin hutu a gidajen ƙasaita a nan, amma muna jin kamar ba abn da suka tsinana. Hukumomi ne a Birtaniya da ba su amfanar kowa sai kansu."

Ba kowa ba ne ke goyon bayan rusa tsarin mulkin sarauta ba. Stephen Allison, tsohon masanin siyasa, maimakon haka sun fi son sake yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima.

"A gaskiya ina son al'adar da ci gaban da manyan sarakuna ke bayarwa amma akwai ƙananan sarakunan da yawa," in ji shi.

"Muna bukatar Sarauniya da Yariman Wales - Ina ma da Yarima William da Yarima George kamar yadda suke kan layin wadanda za su gaji sarautar - amma bayan haka ba ma bukatar tarin Yarimomi da Gimbiyoyi."

"Don haka, ina son na ce na yarda da wasu ra'ayin sarakunan, amma ba duka ba."

Tsarin mulkin sarauta bisa yardar mutanen Burtaniya, kuma a ƴan shekarun nan an ta yin muhawara kan masarautar Burtaniya.

Amma a yanzu, waɗanda ke son kawo ƙarshen masarautar, tsiraru ne.