BBC Hausa of Friday, 23 April 2021

Source: BBC

'Ƴan gudun hijirar da ke kashe kansu saboda mantawa da aka yi da su

Mista Alemi ya ce ya ga mutane da dama da suka kashe kan su Mista Alemi ya ce ya ga mutane da dama da suka kashe kan su

Ali Joya wanda ya rabu da iyaye, da 'yan uwa da abokan arziki, yana daukar abokinsa Mujtaba Qalandari a matsayin dan uwa. Mutanen biyu duka 'yan Afghanistan ne, sun shafe shekaru tare a kasar Indonesia suna jiran samun matsuguni.

"Mutum ne mai karsashi," in ji Mujtaba Qalandari. "Kullum burinsa ya samu matsuguni na dindindin a wata kasa domin ya tallafa wa mahaifiyarsa, wadda take Afghanistan. A kodayaushe yana cewa, ''Ina son sama wa kaina rayuwa mai inganci, na yi aure, na haihu'."

Sai dai Ali ya gaji da jira, a shekarar da ta gabata ya kashe kansa.

Matashi ne yana kan ganiyarsa cikin shekaru 20, kusan shekara takwas yana kokarin ganin ya samu matsuguni.

Mujtaba Qalandari ya kadu matuka.

Ali daya ne daga cikin 'yan Afghanistan 13 da ke kasar Indonesia wadanda suka kashe kansu cikin shekaru uku da suka wuce, kamar yadda Mohammad Yasin Alemi, wanda shi ne kamar wakilin 'yan Afghanistan da ke gudun hijira a birnin Tangerang na kasar Indonesia.

Kowannensu ya shafe shekaru shida zuwa goma yana jiran hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya domin ta fada musu ko an ba su damar samun wurin zama na dindindin. Yawancinsu kuma an yi amanna suna cikin shekarunsu na ashirin.

'Yan gudun hijirar Afghanistan kusan Miliyan 3 ne suka yi rijista da hukumar 'yan gudun hijira a sassa daban-daban na duniya. Rashin cikakken tsaro da rikicin siyasa bayan mamayar da Amurka ta yi wa kasar a shekarar 2001 sun kara ta'azzara matsalar da 'yan kasar ke ciki.

Daga watan Disambar bara, kusan 'yan gudun hijirar Afghanistan 8,000 ne suka yi rijistar neman mafaka da hukumar 'yan gudun hijira a Indonesia, amma kasar har yanzu ba ta rattaba hannu kan yarjejeniyar tsugunar da su da hukumar 'yan gudun hijira ba.

Ba su da damar yin aiki, don haka ba sa iya biyan kudin asibiti da ilimin 'ya'yansu, yawanci suna cunkushe a sansanin 'yan gudun hijira. Yawanci sun shafe gwamman shekaru suna jiran tsammani a kasa ta uku da suke fatan ta ba su wajen zama domin samun ingantacciyar rayuwa.

Birnin limbo ne wurin da Mujtaba Qalandari mai shekara 42 ya yi suna. A shekarar 2015 ne ya yi gudun hijira tare da matar shi da dan su daya, domin gujewa yakin da ake yi Afghanistan da fatan samun intacciyar rayuwa.

Matar shi Gulsum ta kara haihuwar 'ya'ya biyu, mace da namiji a Indonesia. Ta ce zaman jiran ya janyo mu su shiga tsananin damuwa.

"Mun yi rijistar sunayenmu da hukumar 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya tun a shekarar 2015. Amma har yanzu ba bu wanda ya tuntube mu, an manta da," inji Gulsum mai shekara 34. Saboda rashin tuntuba, har yanzu iyalan ba su san makomar su ba, ba su san ko an dauke su a matsayin 'yan gudun hijira ko masu neman mafaka ba.

Mista Alemi ya ce ya ga mutane da dama da suka kashe kan su.

"Babban dalilin shi ne dogon jiran sanin makomarsu. Wadanda ba su yi dogon jira ba su ne masu zaman shekara shida," inji shi.

"Matsalar rashin kudi, da farganbar abin da gaba za ta haifar, da tashin hankali su na kara ingizasu kashe kan su."

Matsalar duk duniya

Can a wani wurin na daban, mutane na jiran shekaru cikin tasku da kunci kafin samun wurin zama.

Akwai akalla 'yan gudun hijira miliyan kusan miliyan daya da dubu dari biyar a duniy da ke tsananin bukatar wurin zana a wasu kasashe, fiye da masu neman mafaka, kamar yadda hukumar 'yan gudun hijira ta bayyana.

Wannan ka iya faruwa ko dai bisa radin kai, ko domin gujewa matsalar tsaro da sauransu.

A shekarar 2019, a duniya ba ki daya akwai 'yan gudun hijira miliyan 26, kuma sama da miliyan hudu su na neman mafaka , kafin annobar cutar korona ta bulla.

Mujtaba Hossain dan Afghanistan ne, wanda ya rasa abokinsa. Matashin mai shekara 22 dakinsu daya da abokin shi Abdul wanda ya shafe shekara bakwai Indonesia.

A wannan lokacin, Abdul mai shekara 36, ya na fatan wata rana sai hadu da matarshi da 'ya'yansa biyu, wadanda bai yi gudun hijira tare da su Indonesia. Amma Mujtaba ya ce a watan Disamba, sai Abdul ya kasa daurewa ya kashe kan shi.

Mutuwar ta girgiza Mujtaba, saboda shi ne kadai abokinsa da ya dauka tamkar dan uwa.

"Mutum ne mai karsashi, ya na da barkwanci, ya na kuma son zuwa motsa jiki." inji Mujtaba. "Mun yi wa juna alkawarin duk inda rayuwa ta kai mu, za mu sake haduwa watarana. Amma ga shi ya bar ni, ni kadai ba ni da kowa."

Har yanzu Mujtaba ya na zaune a Tangerang, a dan tsukakken daki guda, mai 'yar karamar taga inda suke zaune tare Abdul. Ya ce kashi daya cikin uku na ryuwarsa sun tafi a banza, a cikin dn dakin nan da ya ke jiran tsammani.

Wakiliyar hukumar 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya a Indonesia, Ann Maymann, ta shaidawa BBC cewa batun kashe kai da suke yi abin tashin hankali ne, ta kara da cewa: "Abubuwan kalilan ne gwamnati da mazauna yanki da kungiyoyin agaji na duniya za su iya yi."

Maymann ta ce hukumarsu za ta kara inganta kula da lafiyar 'yan gudun hijirar, da wayar da kansu, da kara musu kwarin gwiwa da inganta rayuwarsu. Amma ba ta yi karin bayani kan yadda aikin zai gudana da wadanda za su ci gajiyarsa ba.

Maymann ta bai wa 'yan gudun hijirar shawarar inganta inda suke, amma saboda kasar Indonesia ba ta rattaba hannu kan kudurin hukumar kan 'yan gudun hijira ba , abin da za ta iya kalilan ne.

Yawancin 'yan Afghanistan da ke Indonesia su na fatan ganin sun samu wurin zama a kasa ta uku musamman ma dai kasar Australia. Sai dai kasashen na karbar bakuncin kalilan daga 'yan gudun hijira.

Ma'aikatar harkokin wajen Indonesia ta ce wannan ne dalilin da ya sa mutane ke jiran gawon-shanu a kasashe. Ta yi kiyasin a shekarar 2016, 'yan gudun hijira 1,271 ne suka samu matsuguni a wasu kasashen daga Indonesia, wannan adadin ya kara raguwa a bayan shekara daya. A shekarar 2018 'yan gudun hijira 509 ne suka samu matsuguni.

Musa Sazawar, mai shekara 42, tsohon ma'aikacin gidan talabijin ne daga Afghanistan, ya damu matuka kan adadin wadanda suka samu matsugunin.

Yayin da yake kokarin hadiye kukan da ya taso ma sa, yana kifkifta ido, ya shaida mana cewa a lokacin da ya tsere ya baro matarshi a gundumar Ghazani dauke da karamin ciki.

"Dana zai shekara takwas, amma ban taba ganinshi ba. Ban taba rungumarsa ya ji dumin jikina ba," in ji Musa.

Iyayen Musa ne suka takura kan lallai sai ya bar Afghanistan, bayan barazanar da wata kungiya ke yi ma sa saboda aikinsa na jarida.

"Matata ta ce za ta kula da 'ya'yanmu," in ji Musa. " Gara su girma su samu labarin mahaifinsu yana raye maimakon a mace. Ba na son ka mutu, yarana su tashi a matsayin marayu.'"

Shekara daya bayan ya bar Afghanistan, kungiyar tsaro ta NATO ta kawo karshen aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, Amurka ta janye dakarunta, tashin hankali ya sake barkewa a kasar. Dubban 'yan kasar suka kara fantsama wasu kasashen domin tsira da ran su.

A yanzu da nisan da ke tsakanin Musa da iyalansa ya kai kilomita 8,000, Musa ya dogara ne da wayar salula da amfani da bidiyto na wayar komai da ruwanka domin ganin iyalansa.

"Ba abu ne mai suki ba, ba zan iya dakar kirji na kira kaina uba ba. Amma mecece mafita? Duk matsalolin nan fa sun faru ne saboda gudun hijira da halin da kasarmu ke ciki wanda dole mun zama 'yan gudun hijira wasu kasashe."

Bayan fadi tashin sama wa iyalinshi rayuwa mai inganci, ya ce ba shi da komai face bakin ciki da tashin hankali.

"Tun lokacin da na bar gida da iyalina, na ke cikin kunci da tashin hankali, sakamakon rashin makusanta na," in ji shi.

Wadanda suka taimaka wajen hada rahoton nan su ne: Lesthia Kertopati, Silvano Hajid Maulana da kuma Anindita