Mayaƙan da ke biyayya ga ƙungiyar IS sun yi wa tawagar motocin sojan Najeriya kwanto-ɓauna a Jihar Borno, inda suka kashe mutum 19, ciki har da mayaƙan sa-kai.
Maharan na ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun far wa motocin dakarun ne a kusa da garin Gudumbali da ke yankin tafkin Chadi ranar Alhamis.
Wani jami'an rundunar sojan Najeriya da bai yarda a faɗi sunansa ba ya faɗa wa kamfanin labarai na AFP cewa "mun rasa sojoji guda 15 da kuma mayaƙan sa-kai huɗu a kwanton-ɓaunar da 'yan ta'addan suka yi mana a kusa da Gudumbali".
Ya ƙara da cewa dakarun gwamnati 13 da suka haɗa da soja 10 ne aka jikkata a harin.
Rukunin motocin guda 10 na kan hanyarsu ce ta zuwa Gudumbali daga Kukawa, duka a Jihar Borno, domin ƙaddamar da hari kan 'yan bindigar a lokacin da aka buɗe musu wuta, a cewar wani jami'in sojan.
Ranar Asabar ne Babban Hafsan Sojan Najeriya Lucky Irabor ya isa birnin Maiduguri domin tantance yadda yaƙi da Boko Haram ke gudana a karo na biyu cikin wata shida.
Har wa yau, a Asabar ɗin ne kuma ISWAP ta fitar da wata sanarwa tana iƙirarin kai harin.
Wannan hari shi ne na baya-bayan nan a yaƙin da ya yi sanadiyyar kashe mutum 36,000 kuma ya raba dubban ɗaruruwa da muhallansu a yankin arewa maso gabashin Najeriya cikin shekara 11 da suka wuce.
ISWAP wadda ta ɓalle daga Boko Haram a 2016, na yawan kai hare-hare a Najeriya, abin da ke jawo asarar rayukan sojoji da na fararen hula.